Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta nuna matukar damuwa dangane da halin da ake ciki kan rikicin kasar Yemen, wanda ya fara bayan da al’ummar kjasar suka bukaci shugaba Ali Abdullah Saleh da ya safka daga kan karagar mulkin kasar, inda shi kuma ya yi watsi da wadannan kiraye-kiraye.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta nuna matukar damuwa dangane da halin da ake ciki kan rikicin kasar Yemen, wanda ya fara bayan da al’ummar kjasar suka bukaci shugaba Ali Abdullah Saleh da ya safka daga kan karagar mulkin kasar, inda shi kuma ya yi watsi da wadannan kiraye-kiraye da mutanen kasar ke yi.
Da dama daga cikin mutanen kasar Yemen dai sun yi amannar cewa, wasu daga cikin kasashen yankin musamman ma kasar Saudiyya, tana da hannu wajen kara zuzuta wutar rikin Yemen, domin kuwa shugaba Saleh shi ne babban mai kare manufofin kasashen turai da na larabawa irin su Saudiyya, duk kuwa da yadda suke nuna cewa suna bukatar ya safka.
Kungiyar hadin kan kasashen muslmi ta nuna matukar damuwa dangane da halin da ake ciki kan rikicin kasar Yemen, wanda ya fara bayan da al’ummar kjasar suka bukaci shugaba Ali Abdullah Saleh da ya safka daga kan karagar mulkin kasar, inda shi kuma ya yi watsi da wadannan kiraye-kiraye na al’ummar kasar.
800058