IQNA

Kwamitin Lura Da Zamantakewa A Switzerland Ya Sheda Cewa Kyamar Musulunci Na Karuwa

19:33 - June 22, 2011
Lambar Labari: 2142859
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kula harkokin zamantakewar jama a kasar Switzerland ya fitar da wani rahoto da ke cewa kyamar addinin musulunci da mabiyansa na ci gab ada karuwa atsakanin al’ummar kasar mabiya addinin kiristanci ko yahudanci ko kuma marassa addini.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, kwamitin kula harkokin zamantakewar jama a kasar Switzerland ya fitar da wani rahoto da ke cewa kyamar addinin musulunci da mabiyansa na ci gab ada karuwa atsakanin al’ummar kasar mabiya addinin kiristanci ko yahudanci ko kuma marassa addini da bu yi imani da bin wani tafarki na shiriya ba da suke kasar.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba.
Gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin, na tattare da babban sako.
812431

captcha