IQNA

Kamfanin Jiragen Sama Na Fasaransa Ya Kori Wata Musulma Saboda Saka Hijabi

13:50 - June 25, 2011
Lambar Labari: 2143957
Bangaren kasa da kasa, kamfanin safarar jiragen sam ana kasar faransa ya kori wata ma'aikaciyarsa musulma saboda saka hijabin muslunci da take yi, kamar yadda bangaren kamfanin a kasar Amurka ya bayyana.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na Air France an bayyan acewa, kamfanin safarar jiragen sam ana kasar faransa ya kori wata ma'aikaciyarsa musulma saboda saka hijabin muslunci da take yi, kamar yadda bangaren kamfanin a kasar Amurka ya bayyana a cikin bangaren bayanai kan ma'akatansa.

Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka masana kan harkokin shari'a suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu an kinamincewa da wannan mataki, wannan dai ba shi ne karon farko da mabiya addinin muslunci suke fuskantar matsaloli da kamfanin jiragen sama na kasar faransa ba, domin kuwa hatta fasinjoji da suke mu'amala da kamfanin suna kokawa matyuka.

Kamfanin safarar jiragen sam ana kasar faransa ya kori wata ma'aikaciyarsa musulma saboda saka hijabin muslunci da take yi, kamar yadda bangaren kamfanin a kasar Amurka ya bayyana a cikin wani bayani da ya fiyar.
814166

captcha