IQNA

Wata Tagawa Daga Afrika Za Ta Tafi Gaza Don Taimakawa Fursinonin Palasdinu

17:38 - June 28, 2011
Lambar Labari: 2146059
Bangaren siyasa da zamantakewa; wata tawaga ta Afrika ta kudu da ta kama hanya tun ranar daya ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta isa yankin zirin gaza a wani kokari na goyan baya da taimakawa fursinonin Palasdini da ke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wata tawaga ta Afrika ta kudu da ta kama hanya tun ranar daya ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za ta isa yankin zirin gaza a wani kokari na goyan baya da taimakawa fursinonin Palasdini da ke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra'ila. Akwai irin wannan tawaga daga yankuna da kasashe da dama da ke kokarin ganin sun taimakawa yan uwansu al'ummar Palasdinu da ake gallazawa da take masu hakkoki da kuma dakara su a gidan yari babu wanib dalili balantana bincike yin haka kuma uwa uba babu manyan kasashen dunbiya ko kungiyoyi na kasa da kasa da ke kokarin ganin an kiyaye masu hakkinsu da gwamnatin haramtacciyar kasar isra'ila take take wad a kin kiyaye dokokin kasa da kasa.

814804

captcha