IQNA

Taro Kan wakokin Addinin Muslunci A Kasar Morocco Makonni Biyu Masu zuwa

15:13 - July 30, 2011
Lambar Labari: 2161871
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da shirin taron nan da aka saba gudanarwa akasar Morocco kan warkokin addinin muslunci, da ke samun halartar mawaka na kasar baki daya a karo na goma sha daya, domin raya dararen watan ramadan mai alfarma a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, an fara gudanar da shirin taron nan da aka saba gudanarwa akasar Morocco kan warkokin addinin muslunci, da ke samun halartar mawaka na kasar baki daya a karo na goma sha daya, domin raya dararen watan ramadan mai alfarma a kasar wanda ake gudanarwa bisa kulawar ma’aikatar harkokin addini.
Kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanyar wulaknata abubuwansu masu tsarki, kamar yadda wasu suka dauki irin wannan salo a wasu kasashen nahiyar turai.
Shi dai wannan sojin kasar Birtaniya mai suna Andro Rayan ya sace wani kwafin kur’ani mai tsarki daga wani dakin karatu, inda ya tafi da shi a gaban mutane ya kone shi da wuta, kotun ta ce bisa laifi da aka samu Anro da aikatawa ta yanke masa hukuncin daurin kwanaki saba’in a gidan kaso.
kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanayar wulaknata abubuwansu masu tsarki.
833402

captcha