Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, a cikin wani bayani da ya gabatar babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana hankoron da wasu suke yin a ganin sun kawo baraka a cikin gida ta hanyar bata fuskar gwagwarmayar mutanen kasar, wadda ta kunyata yahudawan sahyniya.
Wannan aya tana magana ga manzon Allah da kuma sauran muminai, tare da tabbatar musu da kadaitar ubangiji wato malamai ma'abuta hankali da ilimi da basira, suna bayyana cewa tsarin da Allah ya yi duniya a kansa da kuma yadda yake tafiyar da wannan tsari, ya isa ya zama babban dalili na samuwar Allah guda daya, wanda hakan kuma gasgata fadar ayar kur'ani mai tsarki ne da ke cewa.
Da a ce akwai wasu alloli a cikin sammai da kassai da tsarinsu ya rushe, da ya daidaice, kasantuwar tsari daya da duniya da sauran halittu suke tafiya a kansa babban dalili ne kan cewa mai tafiyar da tsarin shi ne ya samar da shi, kuma shi kadai ne ya yi abinsa ba tare da taimakon wani ba. Misali kan haka kuwa shi ne, da babu wahadaniyya (kadaitakar ubangiji) da an ga rana na fito ta yamma a wani lokaci, ko ta arewa ko kudu.
Domin kuwa da akwai wasu alloli ba ya ga Allah daya, da kowanensu ya aiwatar da iradarsa wadda ta sabawa sauran allolin, wanda hakan shi ne zai rushe tsari daya da duniya da sauran abin halitta suke tafiya a kansa, rashin samun wannan sabani a cikin tsarin da halitta ke tafiya a kansa, ya tabbatar da cewa wanda ya yi halittar da tsarin duk mahalicci daya rak.
846154