Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na jaridar alwatan da ake bugawa akasar Saudiyya cewa, tarayyar turai za ta gudanar da wani zama na musamman kan batun palastinu inda ake ganin cewa akwai yiwuwar wasu kasha kimanin goma daga cikin kasashen turan su amince da palastinu a matsayin kasa mai cin gishin kanta da ake shirin tattauna batun a babban zauren majalisar dinkin duniya a cikin wannan wata.
A ranar jiya daya ga watan satumba ne aka mikawa kasar Lebanon ragamar shugabancin komitin tsaro na majalisar dinkin duniya na tsawon wata guda, kamfanin dillancin labarun IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, daga jiya Alhamis 1-Satumba-2011 ne kasar Lebanon zata jagorancin komitin tsaro na majalisar dinkin duniya mai membobi 15. Kasar India ce ta jagoranci komitin a cikin watan Aug. da ya gabata.
Komitin dai tana da kasashe 5 masu kujerun din din din, kasashen suna Amurka Britania, Faransa, China da kuma Rasha. Sai kuma wasu kasashe 10 wadanda ake zabe bisa tsarin shiyoyin kasashen duniya na tsawon shekaru biyu kacal.
A halin yanzu kasashen guda goma sune, Lebanon, India, Jamus, Afrika ta Kudu, Brazil, Bosnia Herzogovin, Potigal, Gabon, Colombia da kuma Japan.
853200