IQNA

Ki Moon Ya Bayyana Damuwa Kan Gina Matsugunnai A Cikin Yankunan Palastinawa

14:56 - December 14, 2011
Lambar Labari: 2238827
Bangaren kasa da kasa, babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da gina gidajen yahudawa yan kaka gida acikin yankuynan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamafanin dilalncin labaran kasar Kuwait KUNA cewa, sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da gina gidajen yahudawa yan kaka gida acikin yankunan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan, duk kuwa da cewa babu wani abun da ya yi domin takawa yahudawan birki ba ya magana ta fatar baki.
Ban ki moon dai yana daga cikin masu nuna damuwa kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take danne hakkokin palastinawa, amma kuma a lokaci guda yana nuna matukar tsoro kan abin da ka iya kai ya komo dangane da mukaminsa, saboda haka yana bin salon siyasar harshen damo dangane da sha’anin palastinu.
Babban sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take ci gaba da gina gidajen yahudawa yan kaka gida acikin yankuynan palastinawa da suke gabar yamma da kogin Jordan da yankin Nablus.
914926
captcha