Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Tunisia Musif Marzuki ya bayyana cewa, nasarar da masu kishin islama suka samu a zabukan da aka gudanar a akasashen da aka juyi hakan na nuni da cewa mutane sun amince da cewa Musulunci shi ne mafita.
Kamfanin dillalcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum sabi cewa, shugaban kasar Tunisia Musif Marzuki ya bayyana cewa, nasarar da masu kishin islama suka samu a zabukan da aka gudanar a akasashen da aka juyi hakan na nuni da cewa mutane sun amince da cewa Musulunci shi ne mafita a cikin harkokinsu na siyasa da rayuwa.
A wani labarin kuma shugaban kasar ta Tunusiya ya bayyana cewa; kasarsa a shirye take ta mika tsohon fira ministan Libiya ga mahukunta kasar matukar za a gudanar masa da shari'a ta adalci.
A farkon ziyarar aikin da ya kai kasar Libiya a jiya litinin shugaban kasar Tunusiya Muncif Marzuki ya furta cewa; matukar kasar Tunusiya ta samu tabbacin ma'aikatar shari'ar kasar Libiya tana da cikekken 'yancin da zata gudanar da shari'a ta adalci, to Tunusiya a shirye take ta mika tsohon fira ministan Libiya Al-Baghadadi Ali Al-Mahmudi da yake tsare a gidan kurkukun kasarta ga mahukuntan libiya domin fuskantar shari'a.
Tun a watan Ogustan shekarar da ta gabata ta 2011 ne tsohon fira ministan Libiya karkashin gwamnatin kama karya ta Gaddafi ya tsere cikin kasar Tunusiya bayan da ya ga gwamnatin Gaddafi tana daf da faduwa sakamakon bore da al'ummar kasar suka yi.
928982