IQNA

Juyin Juya Halin Musluncin Iran Abin Koyi Ne Ga Dukkanin Al’ummar Musulmi

20:04 - February 11, 2012
Lambar Labari: 2272289
Bangaren kasa da kasa, juyin juya halin muslunci a kasar Iran abin koyi ne ga dukaknin al’ummar musulmi ta duniya baki daya musamman ma ga larabawa da suke neman sauyi daga mulkin kama karya na shugabanninsu da sarakunansu a cikin wannan zamani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na almajlis.org cewa, shugaban majalisar koli ta musulnuci a kasar Iraki Sayyid Ammar Hakim ya bayyana cewa juyin juya halin muslunci a kasar Iran abin koyi ne ga dukaknin al’ummar musulmi ta duniya baki daya musamman ma ga larabawa da suke neman sauyi daga mulkin kama karya na shugabanninsu da sarakunansu a cikin wannan zamani kamar yadda kowa ya ke sheda hakan.
An gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
Kasashen turai da dama da suka hada da ita kanta kasar Faransa sun matukar damuwa kan makomar wannan juyi da yake faruwa acikin kasashen larabawa a wannan loikaci, domin kuwa abokansu ne akasari aka kawar.
951066

captcha