Bangaren kasa da kasa: cibiyar fitar da bayanai da fadakarwa ta musulmi a garin Toranto na kasar Kanada suna lika sanarwowi da bayanai masu gamsarwa da suka shafi musulmi da addinin musulunci a kokarinsu na yada addinin musulunci da kuma karawa al'ummar kasar ta kanada ilimi da sanin cewa addinin musulunci addini ne na ci gaba da wayewa da zaman lafiya da kuma ke karfawa wajan yada ilimi da zaman lafiya da sulhu a daidaiku da rayuwa da zamantakewa da siyasa da dai sauran bangarori na rayuwa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; cibiyar fitar da bayanai da fadakarwa ta musulmi a garin Toranto na kasar Kanada suna lika sanarwowi da bayanai masu gamsarwa da suka shafi musulmi da addinin musulunci a kokarinsu na yada addinin musulunci da kuma karawa al'ummar kasar ta kanada ilimi da sanin cewa addinin musulunci addini ne na ci gaba da wayewa da zaman lafiya da kuma ke karfawa wajan yada ilimi da zaman lafiya da sulhu a daidaiku da rayuwa da zamantakewa da siyasa da dai sauran bangarori na rayuwa.An nakalto daga majiyar labarai ta mooslym cewa; Muhammad ubaidallah mamba a cibiyar yada labarai da yada addinin musulunci a birnin Toranto cewa: a yarjejeniyar da suka cimma da komitin zirga zirga na birnin na Toronto sun cimma amincewa da fadakar da al'ummar birnin sanin addini na tsawon shekara daya a tashoshin tsayuwa da tashin jirgin cikin karkashin kasa. Kuma suna rubuta wannan sanarwa da ta shafi yada addinin musulunci a cikin harshen turanci da kuma sauran harsuna tamanin da biyar kamar kalamar babu wabi Allah sai Allah kuma Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi manzonsa ne kuma suna bayyana adreshinsu na Internet domin Karin bayani ko kuma gabatar da tambayoyi da suka shafi addinin musulunci.
988695