IQNA

Mutanen Garin Tubli Na Kasar Bahrain Suna Zanga-Zangar Goyon Baya Ga Fursunoni

20:46 - May 10, 2012
Lambar Labari: 2322857
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane a yankin Tubli na kasar Bahrain suna gudanar zanga-zangar nuna cikakken goyon bayansu ga daruruwan fursunonin siyasa da azzaluman sarakunan kasar suke tsare dasu saboda matsayarsu ta siyasa a kasarda ke neman yin adalci a tsakanin mutanen kasar baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na tashar talabijin din Al-alam da ke wata shirinta kan taurron dan adam daga birnin Tehran cewa, dubban mutane a yankin Tubli na kasar Bahrain suna gudanar zanga-zangar nuna cikakken goyon bayansu ga daruruwan fursunonin siyasa da azzaluman sarakunan kasar suke tsare dasu saboda matsayarsu ta siyasa a kasarda ke neman yin adalci a tsakanin mutanen kasar baki daya sabanin yadda ake tafiyar da kasar a halin yanzu.
A wani labarin kuma jaridar Al-Bina ta kasar Labanon ta bayyana cewar gwamnatin Saudiyya tana da hannu dumu-dumu cikin batun makaman da jami'an tsaron kasar Labanon suka kama a kwanakin baya cikin wani jirgin ruwa a tashar jirgin ruwan Trabulus dake arewacin Labanon a hanyarsa ta zuwa hannun 'yan ta'addan kasar Siriya.
Jaridar tace majiyoyi na kurkusa da jami'an tsaron kasar Labanon din sun shaida mata cewa sakamakon binciken da aka gudanar a kan mutanen da ake tsare da su na nuni da cewa gwamnatin Saudiyya ita ce ta ba da kudaden da aka sayi makaman sannan kuma an shigo da su Labanon din ne da shirin yin fasa kwabrinsu zuwa kasar Siriyan.
Kasar Siriyan dai ta jima tana zargin kasashen Saudiyya da Qatar da ba wa 'yan ta'addan da suke kai hare-hare kasar makamai da nufin dagula lamurra a kasar a kokarin da suke yi na kifar da gwamnatin Bashar al-Asad don biyan bukatun kasashen yammaci da kuma HKI.
1003687
captcha