IQNA

Kungiyar Hizbullah Ta Yi Kira Da A Kawo Karshen Rikicin Da Ke Faruwa A Arewacin Kasar

20:54 - May 19, 2012
Lambar Labari: 2329319
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kira da aka wo karshen rikicin da ke faruwa a wasu yankuna na arewa maso kudancin kasar tsakanin masu dauke da makamai wadanda wasunsu ke adawa da Syria wasu kuma na goyon bayanta.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kira da aka wo karshen rikicin da ke faruwa a wasu yankuna na arewa maso kudancin kasar tsakanin masu dauke da makamai wadanda wasunsu ke adawa da Syria wasu kuma na goyon bayanta wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
A wani bayanin kuma kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar da yin Allawadai da babban sakataren majalisar dinkin duniya kan yadda yake nuna halin kom in kula da duk wani batu da ya danganci Palastinu tare da mayar da al’ummar yankin tamkar bayi ga yahudawan sahyuniya ko kuma ba mutane ba.
A wani rahoton kuma daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Lebanon ta Al-intiqad cewa, kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon ta yi kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar mai taken tsaron yahudawan sahyuniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu irin mika wuya da wasu daga cikin larabawa ke yi kai tsaye ga manufofin yahudawan sahyuniya, ya kara tabbatar da cewa dukkanin abin da haramtacciyar kasar Isra’ila take na cin zarafin al’ummar palastinu da sauran larabawa akwai hadin baki tsakaninta da wasu daga mayaudaran gwamnatocin larabawa.
Kungiyar ta hizbullah a kasar Lebanon ba ya ga kakausar suka tare da yin Allawadai da halartar wasu daga cikin kasashen larabawa taron da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta gudanar, ta kirayi iriin wadannan manafukan larabawa da su sake yin nazari kan makomarsu bisa la’akari da halin da ake ciki yanzu haka a yankin.
1010567

captcha