Bangaren kasa da kasa:shugaban jam'iyar musulmi a jamhuriyar Azarbeijan da ake tsare das hi yanzu haka a gidan yari ya fitar da wani bayani cikin kaukausan harshe da bayani cikin bacin rai kan shirin da gwamnati ke son kaddamarwa a wannan kasa da suka sabawa kyawawan halaye tare da yin Allah wadai da wannan shiri.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: shugaban jam'iyar musulmi a jamhuriyar Azarbeijan da ake tsare das hi yanzu haka a gidan yari ya fitar da wani bayani cikin kaukausan harshe da bayani cikin bacin rai kan shirin da gwamnati ke son kaddamarwa a wannan kasa da suka sabawa kyawawan halaye tare da yin Allah wadai da wannan shiri. Muhsin Samdani shugaban jam'iyar musulmi a kasar jamhuriyar musulunci a kasar azarbaijan da ake ci gaba da tsre shi a gidan yari ya fitar da wani bayani wanda a cikinsa yake nuna takaicinsa dab akin cikinsa kan rashin adalci da take hakkokin al'ummar kasar a jamhuriyar musulunci ta Azarbaijan da cewa tayaya ne za a ce a yau sama da shekara guda ana tsare das hi amma kotun kasar ta kasa zama ta saurari irin zargin da ake tuhumarsa das hi domin yanker masa hukumin ko na a ci gaba da tsare shi ko kuma a sake shi . A yau kowa ya san yadda ake kamawa da r=tsare malaman addini a wannan kasa da kuma ci gaba da awan gaba da musulmi a wannan kasa ba tare da yanke masu hukumci da tsare shi a gidan yari kawai don tabbatar da zalunci a kansu ko gabatar da wani dalili da zargi na hankali.
1011257