IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Tura Kwamiti Zuwa mayanmar Domin Ganin Abin Da Ya Faru

14:17 - August 07, 2012
Lambar Labari: 2387790
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta tura wata tawaga zuwa kasar Myanmar domin gane wa idanunta abin da yake faruwa a kasar tare da bayar da rahoton dangane da hakikanin abin da yake faruwa na kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a kasar a cikin yan makonnin nan.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo eurasiareview, cewa kungiyar kasashen musulmi ta tura wata tawaga zuwa kasar Myanmar domin gane wa idanunta abin da yake faruwa a kasar tare da bayar da rahoton dangane da hakikanin abin da yake faruwa na kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a kasar a cikin yan makonnin nan wanda kasashen duniya suka yi gum da bakinsu.
Ko a kwanakin baya Taron kasa da kasa da aka gudanar a kasar Malesiya ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar musulmi a kasar Myanmar wato "Bama". Taron kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malesiya a jiya juma'a ya bayyana kisan gillar da ake yi wa musulmai a kasar Myanmar musamman a jihar Rakhine da cewar take hakkin bil-Adama ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
Da dama daga cikin mahalatta zaman taron sun kuma bukaci daukan matakin matsin lamba kan gwamnatin Myanmar domin ta bada izini ga kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyar hadin kan kasashen musulmi don su kai taimakon gaggawa ga musulmin da suke cikin muwuyacin hali. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ce ta bukaci gudanar da zaman taron, kuma kungiyoyin kasa da kasa kimanin ciki har da Majalisar Dinkin Duniya ne suka halacci taron na gaggawa.
1072354




captcha