IQNA

An fara Gudanar Da Zaman taro Na Ministocin harkokin Wajen Kasashen ‘Yan ba ruwanmu

17:08 - August 28, 2012
Lambar Labari: 2400849
Bangaren siyasa, an fara gudanar da zaman taro na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwanmu a yau nan birnin Tehran tare da halartar ministoci daga kasash sama da tamanin da suka hada da nahiar Asia da ma wasu daga cikin kasashen turai da kuma kudan Amurka da nahiyar Afirka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa an fara gudanar da zaman taro na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwanmu a yau nan birnin Tehran tare da halartar ministoci daga kasash sama da tamanin da suka hada da nahiar Asia da ma wasu daga cikin kasashen turai da kuma kudan Amurka da nahiyar Afirka wadanda suka hada har da manyan kasashe.
A yau ne ministocin harkokin waje na kasashe mambobi a kungiyar ‘yan ba ruwanmu suka fara gudanar da zamansu na share fage babban taron shugabannin kasashensu.
Jim kadan bayan bude taron na yau mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar Izzuddin Ramzi ya mika ragamar shugabancin kungiyar a matsayi na ministocin harkokin waje ga ministan harkokin wajen Iran Ali Akbar salihi.
A cikin jawabin da ya gabatar Izzuddin Ramzi ya bayyana cewa a cikin shekaru uku da Iran za ta rike shugabancin kungiyar, yay i amannar cewa za a samu gagarumin sauyi da ci gaba a cikin dukkanin ayyukan kungiyar. 1086787

captcha