IQNA

Ban Ki Moon Ya Karbi Shawarwarin Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci

23:15 - August 30, 2012
Lambar Labari: 2401910
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya amince da shawarwarin da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya ba shi kan muhimman lamurran da ya kamata ya mayar da hankali kansu da nufin samun adalcia cikin lamurra da suka danganci majalisar dinkin duniya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin ofishin jagora, cewa a yammacin yau ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Ban Ki Moon da ‘yan tawagar da suke rufa masa baya. A yayin wannan ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da irin tsohon tarihi na ci gaba da al'adu da Iran take da shi, ya bayyana cewar: Bisa la'akari da matsayi mai muhimmanci da daukaka da al'ummar Iran suke da shi a fagen al'adu da ci gaba, a saboda haka Jamhuriyar Musulunci ta Iran wani fage mai ne mai kyau na fadada al'adu da ci gaba na dan'adam da ya samo asali daga koyarwa ta Musulunci. A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran ya yi ishara da damuwar da bil'adama suke da ita ciki kuwa har da batun kwance damarar makaman kare dangi inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran dai tana nan daram kan batun kawar da makaman nukiliya daga yankin gabas ta tsakiya, a saboda haka wajibi ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi kokari wajen kawar da irin wannan damuwar dangane da batun makaman kare dangi.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin yadda Amurka da wasu manyan kasashen duniya suka karfafa haramtacciyar kasar Isra'ila da makaman nukiliya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: wannan lamarin babbar barazana ce ga wannan yankin don haka fatan da ake da shi daga wajen Majalisar Dinkin Duniya shi ne ta yi wani abu kan wannan lamarin.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Abin bakin cikin shi ne cewa akwai aibi cikin tsarin majalisar dinkin duniya sannan kuma mafi tinkaho da karfi na duniya wacce kuma take da makaman kare dangi da kuma amfani da shi a baya ita ce take iko da kwamitin tsaron (Majalisar Dinkin Duniyan).
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da jawabin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan dangane da batun kasar Siriya da kuma bukatarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran na taimakawa wajen magance matsalar Siriyan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Lamarin kasar Siriya lamari ne mai sosa rai ainun don kuwa sakamakon shi ne irin yadda ake zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa akidarta da kuma koyarwarta na addini, a shirye take wajen yin dukkanin abin da za ta iya wajen magance matsalar kasar Siriyan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ko da yake a dabi'ance akwai wani sharadi na magance matsalar Siriya wanda shi ne kuwa kawo karshen aikawa da makamai zuwa ga kungiyoyin da ba sa jin suna da wani nauyi a wuyansu a kasar Siriyan.
Jagoran ya ce halin da kasar Siriya take ciki a halin yanzu sakamako ne na aikawa da irin wadannan makamai daga kan iyakoki daban-daban na kasar zuwa ga kungiyoyin da suke adawa da gwamnatin kasar inda ya ce: mallakar makami da gwamnatin Siriya ta yi wani lamari ne da aka saba da shi, don kuwa gwamnatin Siriya kamar sauran gwamnatoci tana da sojoji.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Abu mai sosa rai dangane da lamarin kasar Siriya shi ne cewa wasu gwamnatocin sun tilasta wa gwamnatin Siriyan fada da wasu kungiyoyi da suke adawa da gwamnatin wadanda suke yaki a madadin wadannan kasashen, ko shakka babu wannan yakin shi ne babban matsalar kasar Siriyan a halin yanzu.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wadannan kasashen da suka kirkiri wannan yaki a kasar Siriya, su ne dai suka hana aiwatar da shawarwarin da Kofi Anan ya gabatar, sannan kuma suka hana su samun nasara.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar dai wadannan gwamnatoci suka ci gaba da gudanar da wannan siyasa ta su mai hatsarin gaske a kasar Siriya, to kuwa yanayin kasar Siriya ba zai sauya ba.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da jawaban babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya dangane da batun shirin makamashin nukiliyan Iran inda ya ce: Amurkawa suna da cikakkiyar masaniya cewar Iran dai ba ta nufin mallakan makaman nukiliya, suna fakewa da wannan lamarin ne kawai (don cimma wasu manufofin da suka sa a gaba).
Har ila yau yayin da ya ke ishara da irin gagarumin hadin kan da Iran take ba wa hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Bisa dokokin ita kanta wannan hukumar, wajibi ne ta taimaka wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a fagen ilimi da fasaha, sai dai kuma hukumar kula da makamashin nukiliya ba wai ma kawai ba ta sauke wannan nauyi da ke wuyanta ba ne, face dai a ko da yaushe sai kafar ungulu take yi.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da yadda kasashen yammaci suke fitowa fili su fadi kokarin da suke yi na cutar da Iran ta hanyar internet da suka hada da aikewa da virus din stuxnet zuwa ga na'urori masu kwakwalwa na cibiyoyin nukiliyan Iran, Jagoran ya ce: Me ya sa hukumar kula da makamashin nukiliyan na duniya ba ta dau wani matakin da ya dace kan wannan lamarin ba?
Har ila yau kuma Ayatullah Khamenei ya yi ishara da barazanar da manyan jami'an gwamnatin Amurka suke yi wa shirin nukiliyan Iran inda ya kirayi Mr. Ban Ki Moon din da cewa: fatan da ake da shi shi ne cewa kamata ya yi Majalisar Dinkin Duniya ta dau matakan da suka dace na fada da wannan barazanar.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sake jaddada mahangar Iran dangane da batun haramcin kerawa da kuma amfanin da makaman kare dangi inda ya ce: (Iran ta dauki wannan) matsayar ne bisa tushen akidarta ta addini ba wai don faranta wa Amurka da kasashen yammaci rai ba.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya rufe jawabin nasa ne da gabatar da wata bukata ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan inda ya ce: Dangane da batun kawo karshen makaman kare dangi a duniya, bai kamata ku ji tsoron kowace kasa ba, sannan kuma ka yi amfani da wannan damar da ka samu wajen aiwatar da hakan.
Shi ma a nasa bangaren babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan Mr. Ban Ki Moon ya taya Iran murnar kama shugabancin wannan kungiya ta ‘yan ba ruwanmu kamar yadda kuma ya yi ishara da irin matsayi mai matukar muhimmanci da kuma tasirin da Iran take da shi a wannan yanki inda ya ce: Dangane da batun kasar Siriya a matsayina na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ina kiranjmi da ta taimaka wajen magance matsalar kasar Siriya.
Mr. Ban Ki Moon ya ci gaba da cewa: Mu mun yi amanna da cewa wajibi ne a dakatar da aikewa da makami zuwa ga gwamnatin kasar Siriya da kungiyoyin da suke adawa da ita.
Har ila yau kuma yayin da ya ke nuna damuwarsa dangane da batun shirin nukiliyan kasar Iran, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan ya bukaci kasar Iran da ta kara ba da hadin ka ga hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da kungiyar 5+1.

1088138










captcha