Bangaren kasa da kasa, masu zanga-zangar yin Allawadai da cin zarafin addinin muslunci da wulaknta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a cikin fushi sun afka kan ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tunis inda suka yi bat a kasha da jami'an tsaro.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam, cewa masu zanga-zangar yin Allawadai da cin zarafin addinin muslunci da wulaknta manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a cikin fushi sun afka kan ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tunis inda suka yi bat a kasha da jami'an tsaro a cikin harabar ofishin.
A nasa bangaren jakada na din din din kuma wakilin kasar Iran a MDD Muhammad Khuzaee ya bayyana majigi mai nuna batanci ga addinin Musulunci wanda aka samar a kasar Amurka a kwanakin nan da cewa wani shiri ne na musamman na fada da addinin Musulunci da kuma Musulmi. Khuzaee ya bayyana haka ne a jiya jumma’a a birnin New York na kasar Amurkan kuma ya kara da cewa idan da kasashen yamma musamman Amurka suna bukatar kawo karshen cin mutuncin da akewa iddinin Musulunci da sun yi tun da dadewa. Jakadan ya ce abubuwan da aka yi na nuna batanci ga Musulunci da musulmi ya soma ne tun lokacin da Salman Rushdi ya rubuta wani littafi na nuna batancin ga manzon Allah (s), sannan batun kona Al-qur’ani da aka yi a kasar Amurka ya biyo bayan haka kuma wannan maajigin wanna aka samar a cikin kwanakin nan shi ma a kasar Amurka.
Amma a dukkan wadannan lamura guda ukku gwamnatocin kasashen yamma suna goyon bayan mutanen da suke yin wannan cin mutuncin. Daga karshe jakadan ya bukaci kasar Amurka idan da gaskiya take, tana mutunta sauran addinai to ta hukunta wadanda suka aikata wannan cin mutuncin. Hakama Mohammad Khuzaee ya nemi sauran kungoyin kasa da kasa irin su kungiyar NAM da su fito da su fito da hanyaoyin fada da wannan al-adar ta wulakanta addinai a duniya.
1098043