IQNA

17:38 - September 18, 2012
Lambar Labari: 2414564
Bangaren kasa da kasa, wasu masu tsananin kiyayya da addinin muslunci akasar Amurka sun kaddamar da hari kan wasu masallatai a jahr Virginia ta kasar Amurka da nufin kara tunzura mabiya addinin musulunci domin su dauki wasu matakai na rashin mutunci kan musulmin kasar.

Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ONislam, cewa wasu masu tsananin kiyayya da addinin muslunci akasar Amurka sun kaddamar da hari kan wasu masallatai a jahr Virginia ta kasar Amurka da nufin kara tunzura mabiya addinin musulunci domin su dauki wasu matakai na rashin mutunci kan musulmin kasar musamman a yankunan da suke da yawa.

A wani lokaci a yau din nan litinin ne ake sa ran Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta gabatar wa babban sakataren MDD Ban Ki Moon da wata wasika ta nuna rashin amincewa da kuma yin Allah wadai da shiryawa da kuma yada fim din batanci ga Musulunci da Manzon Allah (s.a.w.a) da aka yi a Amurka.

Yayin da ya ke magana kan wannan lamarin, ministan harkokin wajen kasar Iran Dakta Ali Akbar Salehi ya bayyana cewar ma’aikatar harkokin wajen Iran za ta aike da wannan wasikar da kuma bukatar da a dau matakan da suka dace wajen hana irin wadannan abubuwa da suke nuni da adawa da addinin Musulunci da ke faruwa a kasashen yammaci, kamar yadda ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da tattaunawa da kungiyar hadin kan kasashen musulmi don ganin yadda za a bullo wa wannan lamarin.

A wata sabuwa kuma al’ummar musulmin garin Peshawar na kasar Pakistan sun sanar da lada ta rupia miliyan 10 (kimanin dala dubu 350) ga duk wanda ya kashe wanda ya shirya wannan fim din. Musulmin na garin Peshawar wadanda suka fito zanga-zanga a jiya har ila yau sun bukaci gwamnatin Pakistan da ta fatattaki jakadan Amurka a kasar.

A kasar Afghanistan ma shugabannin kabilu da malaman addini na garin Nangerhar da ke gabashin kasar sun sanya ladar dala dubu 100 ga duk wanda ya kashe wanda ya shirya wanann fim na batanci ga Ma’aiki.

1100228

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: