Kamfanin dilalncin labaran iqka ya habarta cewa, da dama daga cikin masana kan harkokin da suke kai da komowa sun yi imanin cewa bababr manufar fitar da fim din nan na batunci ga manzon Allah tsira da aincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarka it ace bata sunan muslunci a idon uniya tare da bayyana shia matsayin wani addini maras kan gado da rashin tausayi kamar dai yadda hakan shi ne manufar makiya.
A daya bangare kuma shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da rayuwar al'umma, kare 'yancin jama'a, wanzar da doka, zaman lafiya da sulhu sune ginshikan tabbatar da doka a duniya.
A jawabin da ya gabatar a yayin zaman babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 67 kan wanzar da doka a fagen kasa da kasa a jiya litinin; Shugaban kasar Iran Dr Mahmud Ahmadi Najad ya jaddada cewar kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ba zai taba samun nasara a gudanar da ayyukansa ba, saboda matsalar hakkin hawa kan kujerar naki da wasu tsirarun kasashe ke da shi.
Ahmadi Najad ya kara da cewar hakkin hawa kan kujerar naki da wasu 'yan tsirarun kasashe suka kebewa kansu a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi hannun riga da doka, kuma lamari ne da ya hana tabbatar da adalci, hakkokin al'umma da zaman lafiya da sulhu a duniya, tare da jaddada wajabcin bai wa babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karfin gudanar da al'amuran duniya.
Har ila yau shugaban kasar Iran ya tabo shirun da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi kan matsalar makaman nukiliyar da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mallaka, amma a lokaci guda ya sanya matsin lamba kan ci gaban ilimi da wasu kasashe ke samu a fannin ilimin makamashin nukiliya na zaman lafiya.
1106208