Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlas info, cewa an yanke hukuncin daurin shekaru shida a gidan kaso kan wani malamin addinin kirista da ya ci zarafin addinin muslunci abirnin Alkahira na kasar Masar a wani mataki na ladabtarwa gare shi da kuma tamna tsakuwa domin aya ta ji tsoro ga ma duk wani mai tunanin yin hakan a kasar wadda take da yawan musulmi.
A birnin Alkahira dubban mutanen kasar Masar ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani da aka yi a kasar Amurka tare da yin kira da adauiki matakin korar jakadan kasar Amurka da ke zaune a birnin Alkahira saboda rashin saukar matakin da ya dace na kare alfarmar musulunci a kasar.
Wani bangare guda kuma an gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta Masar a jiya.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan babban taro ya kayatar matuka, bisa la’akari da cewa kasar Masar tana da matukar muhimamnci a cikin kasashen larabawa da kuma yankin nahiyar Afirka baki daya, wannane ma ya sanya yanzu haka kasashen larabawa da suke yin amshin shata ga siyasar turawa.
Rahotannin sun tabbatar da cewa, dubban daruruwan mutanen ne suka gudanar da wani babban taron cika shekara guda da samun nasarar juyin juya hali a kasar Masar wanda ya kai ga kifar da gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Husni Mubarak daga mulkin kasar ta masar mai dogon tarihi.
1108672