IQNA

Jagoran juyin musulunci ya bayyana cewa makiya musulunci suna suna yakar farkawarwar musulmi

23:22 - January 29, 2013
Lambar Labari: 2488172
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa makiya addinin musulunci suna suna yakar farkawarwar musulmi ne ta hanyar haifar da rikicin banbancin mazhaba a tsakanin musulmi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da mahalarta taron makon hadin kan al'ummar musulmi na duniya, wanda ya gudana a birnin Tehran kamar kowace shekara a karo na 26, tare da halartar malaman addini da masana daga kasashe 102, inda jagoran ya jaddada wajabcin fadakar musulmi kan wannan babban makirci da makiya suke kitsa musu ta hanyar haifar da fitina a tsakaninsu.

Ya kara kara da cewa idan har makiya suka samu damar haifar da wannan fitina a tsakanin al'ummar musulmi, to kuwa kashe wannan wutar abu ne mai matukar wahala, domin kuwa musulmi za su manta da batun Palastinu da sauran batutuwa da suke gabansu, kuma za su manta da makiyinsu na hakika.

A bangare guda kuma ya bayyana cewa kasashen yammacin turai suna shirin dawo da mulkin mallaka kan al'ummomin Afirka ta hanyar fakewa da wasu dalilai, domin su samu damar sake wawushe dimbin arzikin da Allah ya huwace wa wannan nahiya.

1179826









captcha