IQNA

Juyin Juya Halin Musulunci Na Daga Cikin Muhimman Abubuwa Da Suka Faru A Wannan karni

21:56 - February 09, 2013
Lambar Labari: 2494075
Bangaren siasa, juyin juya halin muslunci na daga cikin muhimamn abubuwan da suka faru a cikin weanann karni kuma yana da bababn tushe a cikin abubuwan da suka tunzura kasashen larabawa wajen farkawar al'ummominsu domin neman yancinsu daga azzaluman sarakuna da shugabanninsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, na'ibin limamin juma'a na Tehran Ayatollah Khatami ya bayyana cewa juyin juya halin muslunci na daga cikin muhimamn abubuwan da suka faru a cikin weanann karni kuma yana da bababn tushe a cikin abubuwan da suka tunzura kasashen larabawa wajen farkawar al'ummominsu domin neman yancinsu.

A gobe ne ake gudanar da tarukan cika shekaru 34 da samun nasarar juyin juya halin muslunci na kasar Iran a dukkanin fadin kasar, inda miliyoyin jama’a za su taru a dukkanin biranan kasar domin nuna murnarsu da zagayowar wannan rana.
A cikin wani bayani da kwamitin kula da shirya tarukan juyin juya hali ya fitar, ya kirayi dukkanin al’ummar kasar zuwa tarukan da za a gudanar gobe idan Allah ya kai mu a fadin kasar, kamar yadda aka saba akowace shekara, miliyoyin mutane ne suke gudanar da wadannan taruka adandalin ‘yanci da ke birnin Tehran, inda shugaba Ahmadi Najad zai gabatar da jawabinsa ga al’ummar kasar.
Kasar Iran ta fuskanci tsangwama daga kasashen turai da kawayensu na yankin, bayan kawar da sarki Shah da ke kare manufofinsu a kasar da ma yankin baki daya, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar Amurka da wasu kasashen turai suka yi ta kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki tsawon shekaru 34, amma hakan bai sanya kasar mika wuya ga manufofin kasashen yammacin turai da na yahudawan sahyuniya ba, inda ta yi amfani da takunkumin da aka kakaba mata wajen dogaro da kanta a dukkanin bangarori, da kuma bunkasa harkokin ilimi da bincike kimiyya da fasaha, lamarin da ya kai ta ga zama daya daga cikin kasashen duniya da suke samun ci gaba cikin sauri, kamar yadda wani rahoto na majalisar dinkin duniya ya tabbatar da hakan. 1185962
captcha