Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da ya gabatar a yayin darasin fikihu mai zurfi a yau jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamrene'i ya bayyana cewa: Hakika makiya sun kai ga tabbaci cewa ba su da karfin halin iya tunkarar al'ummar Iran gaba da gaba, don haka suke kokarin ganin sun raba al'ummar Iran da wannan tsari na Musulunci da Iraniyawan da kansu suka kafa ta hanyar gudanar da juyin juya hali yau tsawon shekaru 34 da suka gabata, amma hakarsu ta kasa kai ga ruwa, don haka wannan ba karamar ni'ima ba ce ta Allah da ya zame wajibi a masa godiya kanta.
Har ila yau jagoran juyin juya halin na Musulunci ya jinjinawa al'ummar Iran kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatansu domin jaddada goyon bayansu ga juyin juya halin Musulunci a ranar bikin cikan shekaru 34 da samun nasarar juyin juya halin da aka gudanar a jiya Lahadi a duk fadin kasar.
Jagoran ya kara da cewar hakika al'ummar Iran sun kunyata makiya ta hanyar fitowarsu jerin gwanon bikin cikan shekaru 34 da kawo karshen mulkin kama karya na gidan sarautar Shah da ya shafe tsawon shekaru 2,500 yana gudana a kasar Iran, domin makiya 'yanci da mutuncin al'ummar Iran ba su taba zaton miliyoyin al'umma zasu fito a yayin jerin gwanon bikin na jiya Lahadi ba.
Haka nan kuma yayin da ya ke kwatanta yadda ake gudanar da bukukuwan zagayowar shekarar nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran da kuma yadda ake yi a wasu kasashen duniya na daban da suka yi juyin juya hali, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: Babban lamarin a nan kasar shi ne cewa al'ummar Iran suna daukan wannan juyi da kuma a wannan kasar a matsayin wata mallaka ta su, don haka suke jin wani nauyi ne a wuyansu su gudanar da irin wadannan bukukuwa. A saboda haka ne suka nuna goyon baya da kuma ba da kariya ga wannan babbar falala wacce ta sama musu daukaka da ‘yanci. Sannan kuma a duk inda bukata ta taso suke bayyanar da kansu.
Ayatullah Khamenei ya gode wa daidaikun al'ummar Iran sakamakon irin wannan fitowa da suka yi don nuna goyon bayansu ga tsarin Musulunci da kuma jagorancinsa inda ya ce: A daidai lokacin da makiya ‘yanci da daukakar al'ummar Iran suke fatan ganin mutane ba su amsa kiran juyin juya halin Musulunci da kuma Jamhuriyar Musulunci ba, amma sai ga shi sun bada wa makiya a kasa a fuska ta hanyar wannan fitowa da suka yi.
Haka nan kuma a wani bangare na jawabin nasa, Jagoran ya yi ishara da kokarin da makiya suke yi wajen rage kaifin irin wannan fitowa da al'ummar suka yi, inda ya ce: Tabbas sun ga hakikanin abin da ya faru, sannan kuma sun fahimci cewa, lalle ba za a iya fada da wannan al'umma ba.
1186615