Bangaren kasa da kasa, gwamnatocin kasashen turai da dama sun nuna damuwarsu matuka dangane da abubuwan da suke faruwa akasashen larabawa inda lamarin ya tashi daga sauya gwamnatoci zuwa tashin hakali da kasashe da rusa al’ummomi da haifar fadan kabilanci da bangaranci da mazhaba.
Kamfanin dilalncin labaran iqn aya habarta cewa, daya daga cikin msana kuma malami a kasashen yammacin turai ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen turai da dama sun nuna damuwarsu matuka dangane da abubuwan da suke faruwa akasashen larabawa inda lamarin ya tashi daga sauya gwamnatoci zuwa tashin hakali da kasashe da rusa al’ummomi da haifar fadan kabilanci da bangaranci da mazhaba tsakanin al’ummomin kasashen, wadanda akasarinsu musulmi ne.
A wani labarin kuma gwamnatin kasar masar ta musanta cewa akwai wani shiri na sauya manya manyan jami'an gwamnatin kasar. Jaridar Misril-yaum ta nakalto kakakin fadar shugaban kasar Masar Yasar Ali yana cewa labarin sauya gwamnatin kasar ba gaskiya ne ba, ya kuma kara da cewa hanyar tattaunawa tsakanin gwamnati da jam'iyyun adawa ce kadai za ta warware halin da ake ciki a kasar.
Yasar Ali ya kara da cewa shugaba Mohammad Mursi zai kira jam'iyyun yan adawar kasar don tattaunawa nan ba da dadewa ba. Shugaba Mursi dai ya yi alkawarin warware matalolin da suka shafi rashin aikin yi, tsaro da talauci a cikin kwanaki 100 na farko a shugabancin sa, amma hakan bai tabbata ba. Gwamnatin Hesham Kandil dai ta kasa aiwatar da alkauran da shugaban ya dauka kusan shekara guda bayan hawarsa kan kujerar shugabancin kasar.
1187490