IQNA

Isra’ila Ita Ce Kan Gaba Wajen Marawa ‘Yan Ta’addan Takfiriyyah Baya A kasar Syria

16:55 - January 31, 2015
Lambar Labari: 2790526
Bangaren kasa da kasa, Jagoran kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrulla a cikin wani bayani da ya gabatar ya bayyana cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ita ce kan gaba wajen taimaka ma ‘yan ta’adda a cikin kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin wilaya da kuma Al-manar cewa, shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar kungiyar Hizbullah tana da hakkin ta mayar da martani ga duk wani wuce gona da iri a kanta da haramtacciyar kasar Isra’ila za ta yi a duk lokaci, waje da kuma hanyar da ta ga ya dace, yana mai cewa: Bayan harin da aka kai wa shahidan Qunetra, mun yi watsi da wani abu mai suna dokokin fito na fito tare da Isra’ila, daga yau babu wani kan iyaka wajen mayar da martani ga wuce gona da irin Isra’ila da kisan gillan da take yi.
Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi wajen bikin girmama shahidan yankin Qunetra da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai musu hari a ranar 18 ga watan Janairun nan, wanda aka gudanar a unguwar Dhahiya da ke birnin Beirut babban birnin kasar Labanon. Sayyid Nasrallah ya ce kungiyar Hizbullah tana cikin dukkanin shirinta sannan kuma babu wani abin da ya same ta sakamakon wannan harin. Sayyid Nasrallah ya ci gaba da cewa: A halin yanzu dai Ista’ilawa sun fahimci cewa lalle shugabanninsu na siyasa da kwamandojinsu na soji wawaye ne a lokacin da suka yanke shawarar kai wannan hari na Qunetra.
Sayyid Nasrallah ya ce: Daga yanzu duk wani daga cikin dakarun Hizbullah da aka kashe, za mu daura alhakin hakan ne a kan Isra’ila kuma ko shakka babu za mu mayar da martani a duk lokaci da kuma wajen da muka ga ya dace.
Yayin da yake magana kan shahidan Qunetran, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar: Haduwar jinin (shahadar) mutumin Iran (yana nufin kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran da yake cikin wadanda suka yi shahadar) da mutumin Labanon (wato shahidan Hizbullah) sannan kuma a kasar Siriya lamari ne da ke nuni da cewa a tafarki guda da ake tafiya.
Shugaban kungiyar Hizbullah ya gode wa al’ummar kasar Labanon da magoya bayan kungiyar da dukkanin wadanda suka taimaka mata musamman mujahidan kungiyar wadanda suka dauki nauyi mayar da martanin da kungiyar ta yi ga wannan harin wuce gona da iri na haramtacciyar kasar Isra’ila, kamar yaddda kuma ya gode wa iyalan shahidan saboda hakurin da suka nuna.
Yayin da ya koma kan asalin harin Qunetran kuwa, Sayyid Nasrallah ya bayyana harin da cewa wani kisan gilla ne da jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila suka tsara shi sannan kuma da sanin manyan jami’ai da kwamandojin sojin haramtacciyar kasar aka kai shi.
Sayyid Nasrallah ya ce: Harin Qunetran wani hari ne da aka cimma matsaya kansa tsakanin manyan jami’an Isra’ila, don haka wani hari ne na kisan gilla a tsakar rana. Don haka Sayyid Nasrallah ya ce tun ranar farko jagororin kungiyar Hizbullah din suka dauki matsayar mayar da martani kan wannan kisan gillan.
Yayin da yake magana kan mayar da martanin da kungiyar Hizbullah din ta yi ga wannan harin na Qunetra a yankin Sheb’ah na kasar Labanon da yahudawan suka mamaye, Sayyid Nasrallah ya ce dakarun Hizbullah sun kai wannan hari na mayar da martani ne a daidai lokacin da sojojin sahyoniyawa suke cikin shirin ko ta kwana; hakan ne ya sanya sahyoniyawan cikin damuwa.
Sayyid Nasrallah ya bayyana haramtacciyar kasar Isra’ilan a matsayin raguwa wacce ta gagara fitowa fili ta sanar da cewa ita ce ta kai wannan hari na Qunetra, alhali kuwa kungiyar Hizbullah tun daga lokacin da ta kai harin Sheb’ah ta dauki nauyin wannan harin a matsayin mai da martani ga harin Qunetran.
Sayyid Nasrallah ya ce babu yadda za a yi Isra’ila ta ci gaba da kashe mutane alhali ita kuma ta ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali.
Sayyid Nasrallah ya ce kungiyar Hizbullah dai ba ta son yaki amma ba ta tsoronsa, sannan kuma a shirye take ta fuskanci haramtacciyar kasar Isra’ila a duk lokacin da ta yi kokarin wuce gona da iri sannan kuma cikin yardar Allah za ta yi nasara a kanta.
A ranar 18 ga watan Janairun nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hari kan yankin Qunetra da ke yankin Tuddan Golan na kasar Siriya inda dakarun kungiyar su shida, ciki kuwa har da dan tsohon babban kwamandan sojin kungiyar shahid Emad Mughniyya, wato Jihad Emad Mughniyya, suka yi shahada tare da daya daga cikin kwamandojin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Birgediya Janar Muhammad Ali Allahdadi.
Tun bayan wannan harin, kungiyar Hizbullah ta yi alkawarin daukar fansa kan wannan harin lamarin da ya tabbata ranar Larabar da ta gabata, 28 ga watan Janairun nan inda dakarun Hizbullah din suka kai hari kan ayarin motocin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin Sheb’ah na kasar Labanon da sahyoniyawan suka mamaye inda suka tarwatsa motocin sojin da kashe na kashewa da raunata na raunatawa.
2785038

Abubuwan Da Ya Shafa: Nasrullah
captcha