IQNA

Jiragen Al Saud Na Ci Gaba Da Rusa Masallatai Da Jigade A Sa’adah

23:32 - April 13, 2015
Lambar Labari: 3138522
Bangaren kasa da kasa, Bama-baman masarautar Al Saud da ke samun taimakon Amurka da Isra'ila, sun safka kan masallacin Sufra mai dadadden tarihi a cikin lardin Sa'ada, da ke arewacin kasar Yemen da asubahin yau, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin masallata.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tahsar Alalam cewa, An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Saudiyya da na Yemen a kan iyakar kasashen biyu a yammacin jiya Asabar, kakakin rundunar gamayyar kasashen da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen karkashin jagorancin Saudiyya  ya sanar da cewa; Sojojin Saudiyya sun yi musayar wuta da sojojin gwamnatin Yemen a yankin da ke tsakanin kan iyakar kasashen biyu a yammacin jiya Asabar, ba tare da fayyace irin hasarar rayukan da gumurzun ya haifar ba ko dalilin bullar musayar wutar.

Rahotonni daga Yemen suna bayyana cewar hare-haren wuce gona da iri da jiragen kasar Saudiyya ke ci gaba da kai wa kan yankunan kasar Yemen suna ci gaba da lashe rayukan fararen hula musamman kananan yara da mata tare da wurga rayuwar jama’ar kasar cikin mummunan yana yi.

A ranar asabar da ta gabata jiragen yakin masarautar sun kai irin wannan hari a filin wasa na garin Yarmuk dake arewacin Sana’a babban birnin kasar  lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar fararen hula guda goma,  har ila yau jiragen yakin Saudiyar sun yi lukudar wuta a kan gine-ginan gwamnati da ofishoshin jami’an tsaron kasar ta Yemen a yankin Marib.

A yankin adan kuwa jiragen ruwan yakin Saudiya ne suka yi lugudar wuta a ma’ajiyar alkama da kuma gine-ginan gwamnati dake wannan gari, a gefe guda kuma jiragen yakin na masarautar Al-sa’oud suka hare-hare kan gidajen fararen hula a yankin Sa’adah dake yammacin kasar.

3134320

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha