IQNA

‘Yan Bindiga Kiristoci Sun Kara Kai Wa Musulmin Afirka Ta Tsakiya Hari

23:53 - August 23, 2015
Lambar Labari: 3350580
Bangaren kasa da kasa, yan bindiga mabiya addinin kirista a jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun sake kaddamar da hari kan musulmin kasar tare da kashe mutane 10.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, a ranar alhamis da ta gabata wasu yan bindiga mabiya addinin kirista a jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun sake kaddamar da hari kan musulmin kasar tare da kashe mutane 10 akalla a daga cikin musulmin.

kungiyar 'yan dabar nan kiristoci wato Anti-balaka a kasar Afirka ta tsakiya sun nuna adawarsu da sake buda makabartar musulmi a birnin Bangui. shafin Internet na Afirka Time ya habarta a cewa a jiya magoya bayan kungiyar Anti-balaka sun yi ruwan duwatsu kan Al'ummar musulmi yayin da suka sake bude makabartarsu dake Bangui babban birnin kasar.



A ranar biyar ga watan maris din shekara ta 2013, rikici ya barke a kasar ta Afirka ta tsakiya, bayan faduwar gwamnatin Francois Bozeze.kuma rikicin yayi sanadiyar mutuwar musulmi da dama tare da raba wasu dubunan da mahalinsu.

Haka nan a cikin shekara ta 2014 musulmin kasar sun isa makabartar ne a bisa kariyar Dakarun tsaro kasa da kasa tare da wasu 'yan jaridu na kasar da kuma na ketare.

duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, hakan bai hana 'yan daban na Anti-balaka yin jifa ba kan tawagar ta musulmi wacce ta halarci sake buda makabartar ta a anguwar  Boeing dake shiya ta biyar, bayan da rufe ta a lokacin da yaki ya barke a kasar.

Kasar Afirka ta tsakiya tana da mutane kimanin miliyan 5 kuma kimanin kashi 15 daga cikinsu mabiya addinin muslunci ne.

3350144

Abubuwan Da Ya Shafa: afirka Ta tsakiya
captcha