IQNA

Kotun Masar Ta Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Shugaban ‘Yan uwa Musulmi

23:55 - August 23, 2015
Lambar Labari: 3350581
Bangaren kasa da kasa, wata kotun Port Said a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan shugaban kungiyar yan uwa musulmi a kasar Muhammad Badei.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, kotun Port Said a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan shugaban kungiyar yan uwa musulmi a kasar Muhammad Badei, haka nan kuma hukunci ya shafi Bitati da kuma Safwat Hijazi.

Ita dai wannan kotun manyan laifuka ta birnin Port Said a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan shugaban kungiyar ‘yan uwa musulmi Muhammad Badei, tare da wasu jiga-jigan kungiyar su 18.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a kan Muhammad Badei da sauran mukarrabansa bisa tuhumarsu da hannu a wani hari da aka kai kan ‘yan sanda a garin Port Said 2013, duk kuwa da cewa wannan ba shi ne hukunci na farko a kan wadannan mutane, domin kuwa kotunan sun yanke musu hukunce-hukunce a kan laifuka daban-daban da ake zarginsu da hannu a ciki, daga cikin hukunce-hukuncen har da na kisa.

Wata kotun ta yanke hukuncin kisa kan hambararren shugaban kasar ta Masar Muhammad Morsi 2014, kamar yadda wasu kotunan kuma suka yanke hukuncin daurin rai da rai a kansa a kan laifuka daban-daban da suke zarginsa da ahnnu a ciki, da hakan ya hada da kai hare-hare a kan gidajen kaso a lokacin juyin juya halin da ya kifar da tsohon shugaban kasar Husni Mubarak, tare da fitar da daruruwa ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi da ake tsare da su.

3350133

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha