IQNA

Zanga-Zangar Al’ummar Kasar Bahrain Domin Adawa Da zalunci

18:37 - October 30, 2015
Lambar Labari: 3417487
Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka kirayi al’ummar kasar Bahrain da su gudanar da jerin gwano a kasar musammana yankin Almusalla.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, al’ummar kasar Bahrain sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da zaluncin da suke fuskanta daga mahukuntan kasar.

Al'ummar kasar Bahrain sun gudanar da jerin gwano mafi girma a tarihin kasar, domin tunawa da cika shekaru hudu da fara neman sauyi a kasar ta hanayar lumana, duk kuwa da irin matakan rashin imani da mahukuntan kasar suka domin hana faruwar hakan.

Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta Bahrain ta samara a cikin wani bayani da ta fitar a yammacin jiya, inda ta tabbatar da cewa an gudanar da zanga-zanga fiye da dari da hamsin a sassa daban-daban na kasar, inda akasarin al'ummar kasar suka fito suna jaddada matsayinsu na neman a gudanar da sauye-sauye a cikin salon tafiyar da mulkin kasar, ta yadda al'umma za su zama wani bangare na siyasa, maimakon mulkin mulukiya na danniya a kan al'umma

A ranar sha hudu ga watan Fabrairun shekara ta dubu biyu da sha daya ce al'ummar Bahrain suka fara gudanar da jerin gwanon neman suyi a cikin salon tafanar jerin gwano da gangami domin neman sauyi ta hanyar lumana, inda mahukuntan kasar suka nemi taimakon kasashen domin murkushe fararen hula a kasar da ke jerin gwano na lumana, inda suka kashe da tare da jikkata mutane da dama.

A daya bangaren kuma dubban al’ummar kasar sun gudanar da jerin gwanon a wasu sassa na nuna goyon baya ga sheikh Abdulzahra Almubashir, wanda aka kame a ranar Ashura saboda gudanar da jawabi.

A ranar da aka gudanar da taron Ashura mahukuntan Bahrain sun kame wasu daga cikin masu jawabi da kuma wa’azi da suka hada da Sheikh Abdul Zahra Almubashir, da kuma Mulla Abbas Aljumri.

3415413

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha