Haka nan kuma yayin da yake
jaddada cewa tsaro daya ne daga cikin mafiya girma da muhimmancin bukatu na
al'umma wanda a saboda haka ne ma Alkur'ani mai girma a wajaje daban-daban yayi
ishara da hakan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A halin
yanzu dai batun tsaro ya tashi daga lamari na soji kawai, ya hada har da
bangarori na tattalin arziki, rayuwar al'umma, al'adu, siyasa, zamantakewa da yanayin
tunanin al'umma.
Ayatullah Khamenei ya bayyana
cewa babban nauyin da ke wuyan majalisar koli ta tsaron kasar ta Iran da cewa
shi ne dubi ta kowane bangare dangane da batun tsaro, don haka sai ya ce:
Wajibi ne majalisar koli ta tsaron kasar ta gudanar da wannan babban aiki nata
ta yadda matsayar da majalisar za ta dauka ta zamanto ta ginu ne bisa mahanga
mai kyau wacce take kallon dukkanin bangarori.
Haka nan kuma yayin da yake
ishara da ayyukan daban-daban na majalisar koli ta tsaron kasar, Jagoran juyin
juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Daukar matsayar da ta dace a majalisar
kolin ta dogara ne da samar da yanayin da yayi daidai dari bisa dari da koyarwa
ta juyin juya hali. Don haka kuwa matukar matsayar da aka dauka suka yi hannun
riga da koyarwar juyin juya halin Musulunci, to kuwa ko shakka babu ba za a
sami sakamakon da ake bukata ba.
Jagoran juyin juya halin
Musulunci ya ci gaba da cewa: Akida da kuma matsayar da suka dace da juyin juya
hali da za a dauka, a hakikanin gaskiya a fili suke, su ne kuwa abubuwan da
suka ginu bisa koyarwa da maganganun marigayi Imam Khumaini (r.a).
Haka nan kuma yayin da yake
ishara da kokarin da wasu suke yi wajen sauya asalin tafarkin juyin juha halin
Musulunci, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Marigayi Imam Khumaini (rahamar Allah
ta tabbata a gare shhi) shi ne tushen wannan juyi na Musulunci. A saboda haka
ne maganganunsa wadanda aka tsara su cikin wasu gomomin mujalladai na littafi,
suka zamanto su ne "tushen juyin juya halin Musuluncin".
Haka nan kuma yayin da yake
magana kan abubuwan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya sha nanatawa da ba su
muhimmanci cikin jawabansa a matsayin ‘tushe na asali na koyarwar juyin juya
halin Musulunci', Jagoran ya bayyana cewar: Bisa maganganun marigayi Imam
(r.a), batutuwa irin su ‘matsayin mutane, ‘yancin kan kasa, riko da addini da
kuma koyarwar ta Musulunci, fada da ma'abota girman kai da amfani da karfi na
duniya, batun Palastinu, batun kyautata rayuwar mutane, kula da marasa galihu
da raunana da kuma kawar da talauci su ne tushen wannan juyi na Musulunci,
wanda daga su ne aka samo tushen koyarwar juyin juya halin Musuluncin".
A saboda haka ne Jagoran
juyin juya halin Musulunci ya ce wajibi ne dukkanin matsayar da majalisar koli
ta tsaron kasar za ta dauka su zamanto sun yi daidai da wadannan tushe na juyin
juya halin Musulunci. Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne ingantattun tunani
da koyarwar juyin juya halin Musulunci su zamanto su ne suke da iko a majalisar
koli ta tsaron kasa.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba
da cewa: Tun daga farkon nasarar juyin juya halin Musulunci, wasu mutane ba su
yarda da wannan tunani da koyarwa ta juyin juya halin Musuluncin ba. Wasu ma,
duk da cewa suna cikin gwamnatin, to amma ba su imani da fada da girman kan
duniya ba. Wajibi ne a tsaya kyam a gaban da irin wannan tunanin.
Haka nan kuma yayin da yake
jaddada cewa tsawon shekaru 37 din da suka gabata, a koda yaushe wannan
gwagwarmayar ta kasance tananan, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana
cewar: Koda yake a halin yanzu makiyan suna amfani da hanyoyi na zamani masu
sarkakiya, irin su hanyar amfani da internet wajen yin tasiri cikin al'adu,
imani, zamantakewa da kuma tsaro. A saboda haka ne wannan gwagwarmaya ta fi
zama mai wahala da kuma muhimmanci.
Har ila yau kuma yayin da
yake ishara da irin tasiri mai girman gaske da wadannan sabbin hanyoyi suke yi
tsaro na al'umma ba tare da an fahimta ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar:
Wajibi ne majalisar koli ta tsaron kasar ta ba wa dukkanin wadannan lamurra
muhimmanci da kuma daukar matsayar da ta dace. A saboda haka ne wajibi ne
majalisar kolin ta yi amfani da tunani mai amfani da kuma aiki ba kama hannun
yaro bugu da kari kan amfani da kwarewa da ta ginu bisa tunani irin na juyin
juya hali wajen daukar ingantacciyar matsayar da ta dace wajen fada da wadannan
sabbin hanyoyi da suke barazana ga tsaro da zaman lafiya.
A karshen jawabin nasa,
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana Rear Admiral Ali Shamkhani a
matsayin daya daga cikin kwararrun sojojin da suka taka rawa yayin kallafaffen
yaki sannan kuma ya jinjinawa irin kokari da majalisar koli ta tsaron kasar
take yi da kuma rahoton da ta tsara dangane da abubuwan da ya kamata a yi a
bangarori daban daban.
Kafin jawabin Jagoran dai,
sai dai Rear Admiral Ali Shamkhani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron
kasar Iran din ya gabatar da wani rahoto dangane da ayyukan majalisar koli ta
tsaron kasar inda ya bayyana ‘tsara siyasa, tsara ayyuka da kuma sanya ido a
matsayin ayyuka guda uku na asali na majalisar koli ta tsaron kasa, wanda ya ce
a koda yaushe majalisar ta kasance mai ba da goyon baya da matakan da aka dauka
da suka shafi ci gaban tsarin Musulunci na kasar ta Iran.