IQNA

An Nuna Kaseti Na Karatun Kur’ani Tartili Da Tajwidi

21:05 - February 05, 2016
Lambar Labari: 3480112
Bangaren kasa da kasa, an nuna cikakken daura na karatun kur’ani mai tsarki na tartili da kuma tajwidi na dukkanin kur’ani a baje kolin littafai na duniya a birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Alwatan cewa, ma’aikatar kula da harkokin addinin a masar ta ce an gabatar da kaset 38 na kira’ar tartili da kuma kaset 60 na tajwidi a wannan baje koli.

Bayanin ma’akatar ya ve; duk wanda ya yi sayayyar littafai a dakin da aka keba ma ma’aikatar a wajen baje kolin na kudi da ya kai Pound 150 za a bas hi wasu littafai na addini kyauta, idan kuma ya kai 225, to za a ba shi dauran cikakka ta wannan kaset baki daya a matsayin kyauta.

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta Masar ta ce babbar manufarta ta samar da wannan hanyar ita ce sawwaka ma masu karatu a wannan fage, domin su iya karatu na tartili cikin sauki da kuma tajwidinsa ba tare da wata matasala ba.

Haka nan kuma ma’akatar ta samar da wasu litaffai wadanda za su kara taimakawa wajen tattaunawa atsakanin msulmi da kuma mabiya addinin kirista kana bin da ya hada su, tare da warware rashin fahimtar juna ta hanyar tattauawa.

An bude wannan baje kolin litatfai na duniya a birnin Alkahira a ranar 27 ga watan Janairu,kuma za a kamala a ranar 10 ga Fabrariru, tare da halartar kasashen larabawa 34, da wasu 13 da ban a larabawa ba.

3472975

captcha