
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Religion News cewa, Megil Rezansky daya daga cikin manyan malaman kirista a Amurka ya bayyana cewa, sakamakon nuna kyama ga musulmi a kasar dole ne a gudanar da wannan tattaunawa da kyakyawar niyya.
Ya ci gaba da cewa ko shakka babu abin da yake faruwa kan musulmi a kasar ba abu ne mai kyau ba, saboda haka ya zama wajibi su tattauna da musulmi domin samo hanyoyin shawo kan wannan matsala, tare da wayar da kan masu gaba da musulmi.
Haka nan kuma ya kara da cewa gudanar da wanann tattaunawa za ta kara kusanto da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, tare da sanya wasu abubuwa da za a yi aiki tare akansu a tsakanin bangarorin na musulmi da kirista.
Dangane da lokacin gudanar da ganawar y ace a cikin shekara ta 2017 ne, kuma har yanzu ba a iya tantance kungiyon musulmin da za su halrci zaman ba.
3474502