IQNA

16:58 - February 28, 2016
Lambar Labari: 3480187
Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin manyan malaman wahabiyawa ya bayyana kafirta musulmia matsayin wani babban laifi a cikin addini lamarin da yasa ake tunanin wani dalili ne ya jawo haka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, Abdullah Mutlaq daya daga cikin manyan malaman wahabiyawa ya bayyana kafirta musulmia matsayin wani babban laifi a cikin addini kamar yadda ya bayayna.

Wannan furuci na wannan mutum ya jawo da dama daga cikin masana kan harkokin addini suna mamakin wannan furuci, domin kuwa ya sabawa abin da akidarsa ta wahabiyanci ta ginu a kansa na kafirta al’ummar manzon Allah tare da kiransu kafirai mushrikai yan bidia a da sauransu.

Almotlaq ya furta wadannan maganganu a waje wani taro na malaman wahabiya, kasantuwarsa daya daga cikin malaman wahabiyan kasar Saudiyya, kuma mamba a kwamitin malaman kasar da ke bayar da fatawa.

Babban abin da ake mamaki a kansa shi ne, yadda wanann gawurtaccen bawahabiye yake furta cewa kafirta musulmi bababn laifi ne, alhali hakan yana daga cikin koyarwar babban malaminsu wanda ya dora su kan wannan turba ta kafirta al’ummar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

Yayin da wasu suke ganin cewa hakan wani sabon salo ne na yaudara, bayan da ta’addanci ya addabi duniya, kuma kowa ya gane cewa wahabiyanci su ne tushen duk wani ta’addanci na duniya, kuma kasar Saudiyya dama a duniya ita ce aka sani da wanann akida da kuma yada a tsakanin msulmi.

Lamarin ya dame su matuka, kuma ana kiransu yan ta’adda a koina acikin fadin duniya, wannan ya sanya ala tilas su canja salonsu na yada wanann akida ta kafirta al’ummar manzon Allah, kuma wannan yana daga cikin sabon salon yaudara da nuna cewa bas u da alaka da akidar kafirta musulmi.

3478996

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: