IQNA

Sumbuksa Da Kankana Da Soyayyen Abinci Na Daga Cikin Kayan Buda Baki A Jibouti

23:47 - June 19, 2016
Lambar Labari: 3480531
Bangaren kasa da kasa, Nauoin abinci da suka hada da sumbuksa da da kankansa da wasu kayan marmari suna daga cikin kayan buda baki a kasar Jibouti.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kasar Jibouti daya daga cikin kasashen gabacin Afirka, tana fadin kasa murabb’I dubu 23, kuma mutanen kasar kimanin kasha 92 cikin dari mabiya addinin mulsunci ne.

Kasar Jibouti tana aladu da dama musamman wadanda ake gudanarwa a cikin watan azumi, wanda hakan ya hada kayan abinci da mutane sukatnada a lokacin buda baki, daga ciki kuwa har da abincin sombuksa da kuma kankana gami wasu daga cikin nauoin kayan marmari.

Bayanin y ci gaba da cewa kasantuwar wannan kasa tana daga cikin kasashen musulmi da addinin muslunci ya yi tasiria acikinsu, wata azumun ramadaman mai alfarma yana babban matsayi a wajen al’ummar wannan kasa.

Sau da dama akan fara tanadin abin da z a yi buda baki da shi a bayan la’asar, kuma kasantuwar kasar tana da kayan marmari, suna samar da su masu tarin yawa domin amfani da su a wannan lokaci.

Haka nan kuma masu yin abinci da za a iya dauka a tafi da shi, wadanda ske yin abinci kamar sombuksa da makamantansa sn fi samun ciniki, domin shi binci ne marassa nauyi da kuma ya dauke da komai.

3508162

captcha