Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na ofishin jagora cewa, a yammacin yau Asabar ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana ta kusan sa'oi biyar da wasu gungun daliban jami'oi na Iran da suka hada da wakilan kungiyoyi daban-daban na daliban jami'a inda suka bayyana wa Jagoran irin matsalolin da suke fuskanta da kuma mahangarsu kan batutuwa daban-daban da suka hada da al'amurran da suka shafi al'adu, zamantakewa, siyasa da tattalin arziki, sannan kuma suka saurari mahangar Jagoran kan batutuwa daban-daban irin su lamurran da suka shafi daliban jami'an, nauyin da ke wuyan daliban jami'an da sauran batutuwa na yau da kullum.
Jagoran ya fara jawabin nasa ne da bayyana cewa ganawar da yake yi a awatan Ramalana da daliban jami'ar wani lamari ne mai dadi da faranta rai inda ya ce: Batutuwa daban-daban da aka gabatar a yayin wannan ganawar, abubuwa ne masu kyau da faranta rai kuma lamari ne da ke nuni da irin ci gaban da daliban jami'a suka samu a fagen tunani, kamar yadda kuma yake nuni da irin yadda kauna da tunanin juyin juya hali ya samu gindin zama a tsakanin daliban jami'a.
Jagoran ya kirayi daliban jami'an zuwa ga riko da Alkur'ani da addu'oin (da aka samo su daga wajen Ahlulbaiti) inda ya ce: Babbar kiran da nake yi wa daliban jami'a ita ce zuwa ga karfafa imaninsu, don kuwa ta hanyar karfaffen imanin ne za su iya fuskantar dukkanin matsaloli da kuma fada da hakan.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kwatanta irin yanayi mai muhimmanci da sarkakiya da kasar Iran take ciki da irin yanayin yakin Ahzab a zamanin Manzon Allah (s.a.w.a) inda ya ce: A halin yanzu dukknain masu bautar duniya da tinkaho da karfi na duniya sun hada karfinsu waje guda don fada da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, suka fada da ita ta kowane bangare.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: A irin wannan yanayin, masu raunin imani wadanda watakila ma suka yarda da akidar makiya, suna kashe gwiwan mutane da sanya musu rashin kyakkyawar fata a zukatansu da jin cewa su ba a bakin komai suke ba. To amma mutane masu karfafaffen imani, komai wahalar da aka shiga su kan yi tsayin daka.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Matukar muna son tsayin daka da kuma tinkarar ma'abota girman kai da kuma kai wa matsayi na daukaka da girman da ya dace da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, to kuwa akwai bukatar karfafa tsoron Allah cikin dabi'unmu na daidaiku da kuma na al'umma.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin matsalar lalacewa da wasu al'ummomin da suka gabata suka fuskanta, kamar yadda Alkur'ani mai girma ya bayyana, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: "Wasa da salla" da "Bin sha'auce-sha'auce" su ne abubuwa guda biyu da suke raunana tsayin dakan da gwagwarmayar da ake yi.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya nake yawan jaddadawa jami'ai da su guji shirya tafiyar yawon shakatawa ta daliban jami'a da ake hada maza da mata waje guda, don kuwa rashin kula da kan iyakoki na addini, lamari ne da ke raunana imanin da mutum yake da shi.
Bayan bayanin gudummawar imani wajen tsayin dakan mutane, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya koma kan batun gwagwarmaya da fadar da al'ummar Iran suke yi da ma'abota girman kai na duniya inda ya ce: Wannan rikici da gwagarmaya ta faro ne daga lokacin da al'ummar Iran suka kuduri aniyar neman ‘yancin kansu da kuma ciyar da kasarsu gaba, wanda hakan yayi hannun riga da manufofin ma'abota girman kan duniyan.
Ayatullah Khamenei ya bayyana maganganun da wasu suke yi na cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman wasu abubuwan da za ta fake da su ne don fada da masu tinkaho da karfi na duniya a matsayin wata magana ta wauta inda ya ce: Wannan gwagwarmayar ba ta bukatar wani abin da za a fake da shi, don kuwa matukar dai al'ummar Iran tana nan a kan tafarkin tabbatar da daukaka da kuma riko da tafarkin juyin juya hali da kuma Musulunci, to kuwa wannan gwagwarmaya tana nan. Hanyoyi biyu ne kawai za su kawo karshen hakan: Ko dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai matsayin karfin da masu adawa da ita ba za su iya tunanin kawo mata hari ba ko kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da mutumcinta ta zamanto ‘yar amshin shata.
Haka nan yayin da yake jaddada cewar al'ummar Iran ta zabi tafarkin farko ne, wato samun karfin da makiya ba za su yi tunanin kawo mata hari ba, wajen kawo karshen wannan fito na fito da ake yi, Jagoran ya ce: Mai yiyuwa ne a halin yanzu siyasar Amurka ita ce kokarin haifar da rikici da rarrabuwan kai tsakanin jami'an gwamnatin Iran da tarraba su a matsayin jami'ai na kwarai da wadanda ba na kwarai ba. To amma matukar dai Amurkawa suka sami dama, to hatta wadannan jami'an da take bayyana su a matsayin na kwarai din za su yi fada da su.
Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar babbar manufar makiyan al'ummar Iran ita ce fada da asali da tushen tsarin Musulunci ta Iran, inda ya ce: Abin nufi da tsarin Musulunci, shi ne gungun abubuwan da suka kafa gwamnatin da kuma manufofi da koyarwar tsarin irin su tabbatar da adalci, ci gaban ilimi, kyawawan halaye, girmama ra'ayin mutane, girmama doka da kuma tafarkin da ake kai.
Haka nan yayin da yake bayyana cewar akwai matsaloli masu yawa da za a iya fuskanta yayin riko da wannan tafarki na gwagwarmaya wadanda za a iya maganinsu ta hanyar tsayin daka da tunani mai kyau. Jagoran ya ce: Lalle daliban jami'a a matsayinsu na wani bangare na karfin da al'ummar Iran suke da shi, suna da rawar da za su taka a wannan bangaren.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana gabatar da bukatun da daliban jami'an suke da su a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske yana mai cewa: Magance manyan matsalolin da ake fuskanta a kasa aiki ne da ke wuyan manyan jami'an gwamnati, to amma bukatun da dalibai suke gabatarwa matukar dai sun ginu bisa tushe na hakika da kuma bincike, ko shakka babu lamari ne da zai share fagen karin kokarin jami'ai wajen magance su.
Daga nan kuma sai Jagoran ya koma kan wasu daga cikin batutuwan da daliban jami'an suka gabatar a jawabin na su.
Yayin da yake ishara da wasu maganganun da daliban jami'an suka yi yayin da suke sukar wasu matakan da aka dauka a jami'oi inda ya ce: Bisa kundin tsarin mulki da kuma hankali, Jagora ba zai iya tsoma baki cikin dukkanin matakai da tsare-tsaren da gwamnati take dauka ba. Idan har jami'ai suka yi kuskure, to wajibi ne majalisa ta yi amfani da karfin da take da shi na sanya ido da suka da hakkin da suke da shi na tsige jami'ai, wajen gyara hakan, ko kuma shugaban kasa yana iya shigowa da gyara hakan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Koda yake a duk inda Jagora ya ga cewa an dauki wani matakin da zai haifar da kaucewa daga tafarkin juyin juya hali wajibi ne ya shigo cikin lamarin da kuma hana aiwatar da shi.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana daliban jami'an a matsayin wata dama mai girma kana kuma daya daga cikin bangaren karfi na gwamnatin Musulunci ta Iran, don haka sai ya kirayi jami'an gwamnati zuwa ga ba da muhimmancin ga jami'an da kuma magance musu matsalolin da suke fuskanta.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kirayi daliban jami'an zuwa ga ba da himma wajen karatunsu a daidai lokacin da suke kuma ba da himma ga batun karfafa imaninsu da Allah da kuma dukkanin abubuwan da za su kusata su ga Allah Madaukakin Sarki. Jagoran ya ci gaba da cewa: Har ila yau kuma wajibi ne daliban jami'an su zamanto ma'abota basira, sannan kuma su zamanto masu sanya ido kan abubuwan da ke gudana a cikin jami'a da kuma batutuwa da suka shafi kasa da kuma ma duniya baki daya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewar: Matukar idanuwa ba su kasance a bude ba sannan kuma ba a yi amfani da basira ba, mai yiyuwa ne daliban jami'a su yi kuskure cikin matsayar da za su dauka cikin lamurran da suke faruwa a wannan yankin da ma duniya.
Jagoran ya kirayi daliban jami'an da su sanya ido sosai kan kafafen watsa labaran makiya yana mai cewa: Makiya sun kashe makudan kudade wajen samar da kafafen watsa labarai masu tsananin adawa da gwamnatin Musulunci ta Iran, wanda babbar manufarsu ita ce raunana bangaren karfin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma bayyanar da wasu bangarori na raunin da ake da su don kashe gwiwa da raunana irin kyakkyawar fatan da ake da shi tsakanin al'umma da matasan kasar nan.
Yayin da yake ishara da irin yadda wadannan kafafen watsa labaran suka yi gum da bakinsu kan irin gagarumar fitowar da al'umma suka yi yayin gudanar da jerin gwanon Ranar Qudus ta duniya a matsayin daya daga cikin misalan irin wannan aiki na kafafen watsa labaran kasashen yammacin, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: A hakikanin gaskiya irin ftowar da mutane suka yi wajen jerin gwanon ranar Qudus a wannan juma'ar duk kuwa da zafin rana da ake fada da shi sannan kuma ga shi suna azumi wani lamari ne mai ban mamaki. To amma kafafen watsa labaran yammaci sun yi gum da bakinsu kan wannan lamari mai ban mamaki, sun ki su bayyana shi. Alhali kuwa idan da wani abu ne mai muni ya faru, da ka ga irin yadda za su kambama shi.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wasu nasihohi guda 12 ga daliban jami'an a matsayin wasu abubuwan da ya kamata su sa a gaba yayin karatu da kuma gudanar da ayyukansu.
Nasiha ta farko da Jagoran yayi musu ita ce amfani da tunaninsu wajen magance matsalolin da ake fuskanta a kasa da kuma shigo fage da kansu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Jagoran ya kirayi kungiyoyin daliban jami'an da su bayyanar da mahangarsu a fili dangane da lamurra masu muhimmanci da suka shafi kasa da kuma riko da tafarkin juyi da suke da shi yana mai cewa: Matukar aka bayyanar da irin wadannan mahanga a fili, hakan lamari ne da zai karfafa masoya wannan juyin sannan kuma makiya ciki kuwa har da Amurkawa za su fahimci cewa bai kamata su yi farin ciki ba dangane da irin gurbatattun rahotannin da ake ba su kan matasan Iran.
Ayatullah Khamenei ya bayyana "yarjejeniyar nukiliya", "alaka da Amurka", "siyasar tattalin arziki na dogaro da kai" da kuma "makomar kasar Iran" a matsayin wasu daga cikin lamurra masu muhimmanci, don haka ya kirayi kungiyoyin daliban jami'an da su sanar da matsayarsu da suka yi daidai da koyarwar juyin juya halin Musulunci kan wadannan lamurra kuma a fili.
Nasiha ta biyu da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa daliban jami'an ita ce "Yin bayani da kuma kokarin kwantar da hankalin zukata".
Jagoran ya bayyana cewar: A koyarwar Musulunci, janyo hankula da neman yardar zukata wani lamari ne mai muhimmancin gaske. A saboda haka wajibi ne kungiyoyin daliban jami'a, ta hanyar amfani da karfafan hujjoji, su yi wa daliban jami'oi bayanin matsayarsu.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana batutuwa irin su "siyasar tattalin arziki na dogaro da kai, ci gaban ilimi, tsarin rayuwa mai sauki da kuma alaka da Amurka" a matsayin batutuwan da suke bukatuwa da baynai da kuma bayyanar da mahangar daliban jami'a kansu.
Dangane da batun alaka da Amurka, Jagoran ya bayyana cewar: Yana da kyau kungiyoyin daliban jami'a su yi tunani kan wasu mahanga da matsalar Jagora kan batutuwa irin su "kin amincewa da kulla alaka da Amurka da kuma kore tattaunawar da ita in dai ba kan wasu ‘yan tsirarrun batutuwa ba", sannan ta hanyar nazarin karfafan hujjojin da aka gabatar kan wadannan lamurra su yi bayanin su ga sauran daliban jami'a da suke tare da su.
Nasiha ta uku da Jagoran yayi wa daliban jami'an ita ce kokari wajen "kara irin fahimta ta siyasa da ta addini da suke da ita.
Nasiha ta gaba da Jagoran yayi wa daliban ita ce "Fitowa fili wajen kare tsarin Jamhuriyar Musulunci ba tare da wani noke-noke ba".
Jagoran ya bayyana cewar: Makiya suna amfani da wasu rauni da gazawar da ake da su wajen bayyanar da juyin juya halin Musulunci a matsayin wani tsari da ya gaza a daidai lokacin da suke rufe ido kan irin ci gaba da nasarorin da aka samu. A saboda haka ya zama wajibi kungiyoyin daliban jami'a su dagula musu lamurra a wannan rashin adalci na su.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tsayin daka a gaban irin wannan kiyayya ta tsawon shekaru 37 ta makiya a matsayin mafi muhimmancin nasarar da gwamnatin Musulunci ta Iran ta samu, shi din ma a irin wannan yanayin da hararar irin wadannan manyan kasashen duniya ga daya daga cikin hukumomin gidan sarauta kawai ta isa ta tilasta musu mika kai.
Nasiha ta shida da Jagoran yayi wa daliban jami'an ita ce ci gaba da riko da kuma karfafa tafarkin ba da gudummawa da agaji da al'ummomin karkara musamman yankunan da suke fuskantar matsaloli na rashi.
"Kula da tsarin rayuwa mai sauki wacce ta dace da al'adar al'ummar Iran da kuma koyarwa ta Musulunci" da kuma "karfafa akida da koyarwar juyin juya halin Musulunci da suka hada da tattabar da adalci, karfafa tattalin arziki, ci gaban kasa da kuma ilimi" su ne nasihohi na bakwai da na takwas da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa daliban jami'an.
Dangane da hakan Jagoran ya bayyana cewar: Ni dai koda wasa ban yardar da irin ci gaban kasashen yammaci ba, don kuwa ba su ginu bisa tushe na kwarai ba. A saboda haka ne na gabatar da batun ci gaban irin na Musulunci da kuma Iran.
Nasiha ta tara da Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi wa daliban jami'ar ita ce "Kafa wani sansani guda na fada da Amurka-Sahyoniyawa a tsakanin daliban jami'oin duniyar musulmi"
Jagoran ya ce: Za a iya amfani da irin kafafen watsa labarai na zamani da ake da su wajen kirkiro wani kamfain da wani shiri na nuna adawa da bakar siyasar Amurka da yahudawan sahyoniya a tsakanin daliban jami'an kasashen musulmi. Wanda ta hakan ne miliyoyin daliban jami'oin kasashen musulmi za su bayyanar da mahanga da matsayarsu da kuma samar da wani gagarumin yunkuri a duniyar musulmi.
Nasiha ta goma da Jagoran yayi wa daliban jami'an ita ce "nesantar zargin wasu da rashin riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, don kawai ra'ayinsu ya saba da irin wanda suke da shi.
"Karfafa alaka tsakanin kungiyoyin daliban jami'a masu riko da tafarkin juyi ta hanyar dogaro da abubuwan da aka yi tarayya kansu" ita ce nasiha ta goma sha daya da Jagoran yayi wa daliban jami'an. Jagoran ya ce bai kamata sabanin da ake da shi ya zamanto abin da zai haifar da rikici da tada jijiyoyin wuya a tsakanin daliban jami'an ba.
"Dubi da idon basira ga koyarwar juyin juya halin Musulunci da kuma tunani kan makomar kasar Iran" ita ce nasiha ta karshe da Jagoran yayi wa daliban jami'an a yayin wannan ganawa ta su.
Jagoran ya bayyana cewa makomar kasar Iran tana hannun daliban jami'an ne wadanda a nan gaba su ne za su zamanto shugabannin kasa, ‘yan majalisa da sauran jami'an kasar, a saboda haka ya kiraye su zuwa ga yin tunani da kuma yin tsari na ciyar da kasa gaba.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da irin mummunan tajrubar da al'ummar Iran suke da ita kan irin abubuwan da kasashen yammaci suka yi musu da suka hada da tilasta musu mulkin kama karya na ‘ya'yan gidan sarautar Pahlawi, kifar da gwamnatin da mutane suka zaba, kafa ‘yan sandan Savak masu azabtar da mutane. Don haka sai ya ce: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, kiyayyar farko da aka nuna wa al'ummar Iran da suka hada da sanya takunkumi, ha'inci, leken asiri, bakar farfaganda, goyon bayan kungiyoyi masu adawa da juyin juya halin Musulunci, kallafawa Iran yaki na shekaru takwas, goyon bayan Saddam, harbo jirgin saman fasinjar Iran zuwa ga karya alkawurra da sauran, dukkanin wadannan abubuwa da kasashen yammaci musamman Amurka suka aikata.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin mummunan aikin da kasar Farasan da Amurka suka yi a yayin tattaunawar nukiliya da aka yi da Iran, Jagoran ya bayyana cewar: A yayin wannan tattaunawa ta nukiliya ya tabbata cewa Amurkawa da suka hada da majalisa da gwamnati, suna kan kan kiyayyar da suke yi da al'ummar Iran.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Hankali dai yana hukunta cewa wajibi ne a yi amfani da hankali da kuma hikima wajen tinkarar irin wadannan makiyan sannan kuma kada mu bari mu fada tarkon yaudararsu.
Haka nan kuma yayin da yake mayar da martani da ikirarin Amurkawa na cewa suna son tattaunawa da irin kan batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta tsakiya da kuma aiki tare ciki kuwa har da batun kasar Siriya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Mu dai ba ma son irin wannan aiki taren, don kuwa babbar manufarsu ita ce kawo karshen tasirin Iran a yankin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana adawa da tsoma bakin da Amurka take yi cikin lamuran kasashen yankin Gabas ta tsakiya.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Ni dai bisa nauyi na addini da shari'a da kuma dan'adamtaka da ke wuyana, lalle matukar dai ina raye zan ci gaba da tsayin daka kuma lalle na yi amanna da mutane, kamar yadda kuma na ke da yakini kan sakamakon wannan tsarin dakan wanda shi ne samun nasara.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da wasu mutane 8 daga cikin wakilan kungiyoyin daliban jami'an suka gabatar da jawabinsu inda suka gabatar da mahangar kungiyoyin nasu kan batutuwa daban-daban da kuma matsalolin da suke fuskanta bugu da kari kan hanyoyin da suke ganin za a iya bi wajen magance wadannan matsalolin.
Daga karshe dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jagoranci mahalarta taron sallar magariba da lisha kana daga karshe kuma suka yi buda baki tare.