IQNA

Khalifan Darikar Muridiyyah:

Marigayi Imam (RA) Da Juyin Islama Na Iran Na Cikin Ran Al’ummar Senegal

23:40 - November 01, 2016
Lambar Labari: 3480897
Bangaren kasa da kasa, sheikh Mukhtar Mbaki shugaban darikar muridiyyah a yayin ganawa da babban sakataren cibiyar Ahlul bait (AS) Hojjatul Islam Muhammad Hassan Akhtari ya yabi Imam (RA) da juyin Iran.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar Ahlul bait (AS) cewa, an gudanar da taro a kasar Senegal wanda ya samu halartar babban sakataren cibiyar Ahlul bait (AS) inda aka tattauna muhimman batutwqa da ska alaka ta addini da al’adu tsakanin Iran da Senegal tare da babban malamin darikar muridiyyaha kasar sheikh Mukhtar Mbaki.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taron akwai Ramezani Khani mataimakin babban sakataren cibiyar Ahlul bait (AS) da kuma Haji Ali Zadeh shugaban bangaren Afirka na wannan cibiyar.

A yayin ganawa da tawagar Iran da kuma babban malamin darikar muridiyyah sheikh Mukhtar Mbaki, an tattauna irin alakar da ke tsakanin wannan gida na sufanci da kuam kasar Iran, wadda ta shahara wajen yawan malamai masana harkar sufanci.

Haka nan kuma jakadan Iran Kashkawi da kuma Sayyid Hassan Islamti shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na Iran a Senegal, saikuma Mu’atkidi shugaban reshen jami’ar Almustafa (SAW)a kasar, wadanda suka kasance daga cikin masu kyakyawar alaka da gidan darikar muridiyya.

Bayan kammala tatatunawar sun ziyarci hubbaren babban shehin darikar ta muridiyyah sheikh Ahmadu Bamba, daga nan kuma suka wuce zuwa babban ginin hukumar radiyo da talabijin ta kasar, inda suka gana da jami’aia wurin.

3542002


captcha