IQNA

Jami’an Tsaro Fiye Da Dubu 30 Ne Za Su Yi Aiki A Taron Arba’in Na Imam Hussain (AS)

23:04 - November 11, 2016
Lambar Labari: 3480929
Bangaren kasa da kasa, babban kwamandan rundunar da ke kula da ayyukan tsaro na yankin Furat ya bayyana cewa fiye da jami’an tsro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tshar al’alam cewa, babban babban kwamandan rundunar tsaro da ke kula da yankin Furat Qais Khalaf ya bayyana cewa fiye da jami’an tsro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in na imam Hussain (AS) a shekarar bana.

Yace a halin yanzu haka sun riga sun fara gudanar da yayukansu, domin tabbatar da cewa sun bayar da kariya ga masu gudanar da wannan babban taro na ziyarar arbain na Imam Hussain (AS) a birnin karbala mai alfarma.

Daga cikin ayykan har da kula da zirga-zirgar jama’a da kuam sanya ido kan dukkanin masu kai komo, domin tabbatar da cewa yan ta’adda ba su kawo wani cikas a taron ba.

Haka nan kuma za a kafa wuraren binciken ababen hawa da kuma jama’a a ciki da wajen birnin karbala mai alfarma, kamar yadda kuma wasu dubban masu ayyukan agaji za su hada karfi da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa komai ya tafi cikin tsari.

Kimanin mutane miliyan 15 ne dai akee sa ran za su halarci taron arba’in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.

3545051


captcha