IQNA

Zangon Kur’ani A Kan Hanyar Isa Karbala Daga Najaf

19:37 - November 17, 2016
Lambar Labari: 3480949
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da tattakin da mabiya mazhabar iyalan gidan manzo kiye zuwa Karbala an kafa wasu tantuna na karatun kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, wasu daga cikin tawagar Iraniyaw amsu ziyarar arbain na Imam Hussain (AS) sun yada zangoa wani tanti na karatun kur’ani mai tsarki a kan hnyar Najaf zuwa Karbala.

Daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasar Iraki Ibrahim Albadiri ya yi tilawar ayoyin kr’ani mai tsarkia wurin, kafin daga bisani kuma Abu Tahsin Najjar shugaban masu aikin sa kai na yada karatun kur’ani a tattakin arbain ya gabatar da nasihohi.

An daga tutar hubbaren Sayyidah Fatima Ma’asuma (SA) a cikin wannan tanti na hidima ga kur’ani mai tsarki, inda daga bisani aka bayar da kyautar wanann tuta mai labrka ga masu gudanar da hidima a wannan tanti.

3546692


captcha