IQNA

Dakarun Sa-Kai A Iraki Sun Fattaki Wasu ‘Yan Ta’addan ISIS A Kusa Da Karbala

23:18 - January 26, 2017
Lambar Labari: 3481172
Bangaren kasa da kasa, dakarun sa-kai na kasar Iraki sun fatattakin ‘yan ta’addan ISIS a yankin Rihaliyyah da ke kusa da birnin Karbala.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Iraki na Saumaria News cewa, ‘yan ta’addan na takfiriyya na kungiyar ISIS, sun kaddamar da hari ne a wani wurin tsaro da ke yankin Rihaliya a kusa da birnin Karbala, wanda ke makwaftaka da lardin Anbar, daya daga cikin yankunan da aka fatattaki ‘yan ta’addan ISIS.

Rahoton ya ce dakarun sa kai na Iraki sun samu nasarar halaka wasu daga cikin ‘yan ta’addan, sun kuma jikkata wasu, yayin da wasu kuma suka ranta cikin na kare, kamar yadda wasu daga cikin dakarun na sa kai na kasar Iraki suka samu raunuka, sakamakon musayar wuta mai tsanani tsakaninsu da ‘yan ta’addan takfiriyyah na ISIS.

Tun a cikin shekara ta dubu biyu da sha hudu ce dai mayakan ‘yan ta’addan takfiriyyah tare da taimakon wasu kasashen larabawa da na turawa suka shigo cikin Iraki tare da kame wasu yankunan kasar, da sunan kafa abin da suke kira daular muslunci.

3567153


captcha