IQNA

Shirin Bayar da Horon Fahimtar Ma’nonin Ayoyin Kur’ani A London

23:33 - February 23, 2017
Lambar Labari: 3481254
Bangaren kasa da kasa, bisa la’akari da karatowar watan azumi tsanyar koyar da ilmomin muslunci ta jami’ar Landan za ta shirya wani shiri kan fahimtar ma’anonin kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, shafin yanar gizo na iidr ya bayar da rahoton cewa, wannan shiri na daga cikin shirye-shirye da ake gudanarwa a wannan bangare a lokutan azumin Ramadan mai alfarma.Bayanin ya ce za a gudanar da zama na bayar da horo kan manonin ayoyin kur’ani da ske da alaka da zamantewa da kuma rayuwa, tare da fitar da darussan da ke ciki ga dan adam.

Ranakun da za a gudanar da wannan nzama kuwa su ne 8 da kuma ga watan Ramadan mai alfarma, sai kuma ranakun 15 da kuma 16 ga watan na Ramadan idan Allah ya kai mu.

Wanann shiri dai zai duba surori guda 114 daga cikin kur’ani mai tsarki, kuma malamai da masana za su gabatar da bayanai da laccoci a kan maudu’ai daban-daban da za a ba su.

Babbar manufar wanann shiri dai ita ce kara ilmantar da musulmi kan abubuwan da suke cikin addininsa domin ya aiwatar da su bisa ilimi ya kuma kara karfafa alakarsa da mahaliccinsa bisa ilimi da masani ta hakika.

3577468


captcha