Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Sadiq Kujandi shugaban majalisar muuslmin Burndi ya bayyana cewa, wannan shi nr karon farko da aka tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harshen mutanen kasar.
Ya ci gaba da cewa, wannan babban abin farin ciki ne ga dukkanin muuslmi na wannan yanki, domin kuwa bayan kwashe sekaru 8 a jere ana wannan aikin tarjama, yanzu an kammala.
Ana magana da harshen Rwandi a kasashen Burundi, da wasu yankuna na Tanzania, jamhuriyar dimukradiyyar Congo da kuma Uganda.
Musulmi su ne kashi 10 cikin dari na utane miliyan 11 da e rayuwa akasar Burundi, kuma suna rayuwa e a biranen Gitga, Romunko da kuma Bujumbura fadar mulkin kasar.
Musulunci ya isa Burundi ne a cikin karni na sha tara.