Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, tun a daren jiya ne al’ummar kasar Bahrain a mafi yawan garuruwan kasar, suke gudanar da gangami da jerin gwano, domin tunawa da zagayowar ranar 14 ga watan fabrairu, ranar da suka fara boren neman hakkokinsu da aka haramta musu.
A yau ake cika shekaru bakwai da fara bore da gangami na lumana a kasar ta Bahrain, wanda ke neman a baiwa dukkanin ‘yan kasa hakkokinsu ba tare da nuna wani banbanci ko bangaranci na mazhaba ba, amma masarautar Bahrain ta yi amfani da dukkanin karfinta wajen murkushe al’ummar kasar.
Masarautar kasar Bahrain da ke samun dauki da kuma cikakken goyon baya da taimako daga kasashen Saudiyya, Amurka da kuma Birtaniya, tana bin salon mulkin mulukiya na kama karya ne, inda al’umma basu da hakki a cikin lamurra da suka shafi mulkin kasa ko ‘yanci na siyasa, wanda al’ummar kasar suka kosa da shi.