IQNA

Ministan Ilimi Na Isra’ila Ya Mayar Da Martani Kan Sakamakon Zaben Lebanon

23:51 - May 07, 2018
Lambar Labari: 3482639
Bangaren kasa da kasa, ministan ilimi na haramtacciyar kasa Isra’la ya mayar da martani dangan da sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na Reuters cewa, a lokacin da yake mayar da martani kan zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Lebanon ministan ilimi na haramtacciyar kasar Ira’ila Naftali Bent ya bayyana cewa; nasarar da Hizbullah ta samu ya nuna cewa babu wani banbanci tsakanin Hizbullah da mutanen Lebanon.

Ministan haramtacciyar gwamnatin yahudawan ya ci gaba da cewa, daga yanzu suna kallon cewa da gwamnatin Lebanon da Hizbullah da al’ummar kasar duk abu daya ne, kuma duk abin zai farua  nan gaba, to gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin hakan, domin Hizbullah ta kankane komai a cikin gwamnatin.

Sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Lebanon ya nuna cewa, Hizbulah da abokan kawancenta ne suka lashe mafi yawan kujerun majalisa dokokin kasar.

Wannan lamari dai ya daga hankalin Isra’ila matuka, da ma wasu daga cikin kasashen larabawa da suka kashe biliyoyin dalolin wajen bayar da cin hanci da rashawa domin ganin an kayar da ‘yan takarar Hizbullah a  zaben.

3712107

 

captcha