Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jami’an diflomasiyya fiye da 80 ne daga kasashen duniya aka gayyata domin halartar bikin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin Quds, amma da dama daga cikin sun ki karba gayyatar.
Daga cikin jakadun kasashen da aka gayyata mafi yawan jakadun kasashen turai ba za su halarci wurin ba, da suka hada har da jakadun Jamus, Birtaniya, Faransa da kuma Italia.
A gobe 14 ga watan Mayu ne za a bude ofishin jakadancin na Amuka, wanda aka gina a birnin Quds,a matsayin amincewa da wannan birnin mai alfarma a matsayin fadar mulkin yahudawan Sahyuniya.