Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka saba gudanawa a kasar Keya cikin kowane watan ramadana mai alfarma a birnin Nairobi.
Ofishin jakadancin kasar Iran da ke birnin Nairobi ne dai ya saba daukar nauyin shirya wannan gasar kur’ani a kowace shekara a cikin watan Ramadan.
A wannan karon ma gasar takebanci dalaiban makarantun firamare da sakandare ne, kuma gasar ta kunshi matakai daban-daban, kama daga bangaren hardar dukkanin kur’ani, da kuma kasa da kasa, gami da tilawa da kuma tajwidi.
A yau ne za a bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a gasar.