Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labarai na Saumariyya News cewa, sakamakon wani harin ta’addanci da wasu ‘yan kungiyar Daesh suka kai kan ‘yan sandan Iraki a Samirra wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu yayin da kuma wasu suka jikkata.
Bayanin ya ce wasu ‘yan ta’addan wahabiyawan Daesh ne suka kaddamar da harin akan wani shingen tsaro a garin Samirra, inda suka kasha ‘yan sanda 3 da kum ajikkata wasu 2 na daban.