IQNA

Alaka Tsakanin Iran Da Jami’oin Addini A Kenya

20:30 - July 21, 2018
Lambar Labari: 3482838
Bangaren kasa da kasa, alaka na ci gaba da kara habbaka tsakanin Iran da jami’oin addini na kiristanci da musulunci a kasar Kenya

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalyo daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar bunkasa al’adun muslunci cewa, alaka na ci gaba da kara habbaka tsakanin Iran da jami’oin addini na kiristanci da musulunci a kasar Kenya a cikin lokutan baya-bayan nan.

A yayin wani zama da aka gudanar tsakanin shugabannin jami’oin addini na Kenya da kuma jakadan kasar Iran a kasar a birnin Nairobi, dukkanin bangarorin sun cimma matsaya kan kara bunkasa wannan alaka.

Babbar manufar Iran ta yi hakan dai ita ce kara kusanto da fahimtar una tsakanin mabiya addinai, da nufin kara fadada fahimta juna da zaman lafiya a tsakaninsu.

Dukkanin bangarorin da suka halarci zaman dai sun nuna gamsuwarsu da ci gaba da aka samu ta wannan fuska, tre da shan alwashin ci gaba da bin abin da aka cimmawa.

Tun a shekarar da ta gabata ce aka fara gudanar da irin wannan zama tsakanin Iran da wadannan bangarri a kasar ta enya.

3731933

 

captcha