IQNA

Masarautar Bahrain Ta Hana ‘Yan Aadawa Gudanar Da Harkokinsu

23:57 - August 01, 2018
Lambar Labari: 3482851
Bangaren kasa da kasa, Hamad bin Khalifa Ali Isa sarkin masarautar kama karya ta kasar Bahrain ya kafa dokar hana ‘yan adawa gudanar da komai a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Mir’at Bahrain ta habarta cewa, sarkin masarautar kama karya ta kasar Bahrain ya kafa dokar hana ‘yan adawa gudanar da komai a kasar baki daya.

Rahoton ya ce wannan na zuwa a ci gaba da murkushe duk wani yunmuri na neman hakkokin al’ummar kasar da masarautar kama karya ta kasar take takewa.

Masarautar kama karya ta Bahrain dai na kallon duk wani yunuri na al’ummar kasar da ke neman a yi adalci da yin daidaito a tsakanin al’ummar a matsayin barazana ga mulkin kasar.

Yanzu haka dai ‘yan adawa da dama da dama ne akae tsare da su a gidajen kurkuku saboda ra’ayinsu na siyasa, kamar yadda kuma akwai daruruwan masu fafutkar kare hakkin bil adama da manyan malamai da suke tsare saboda yin kira da suke yi ga masarautar kasar kan ta yi adalci.

3735053

 

 

 

 

 

captcha