Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qaf cewa, a jiya ne aka fara aiwatar da wani shiri na koyar da hardar kur’ani mai taken Imamain a garin Samirra na Iraki a hubbaren da ke birnin.
Wannan shiri dai zai dauki tsawon watanni biyu ana aiwatar da shi, inda dalibai dari ne da suka cika sharudda aka dauka a matsayin zangon farko na shirin.
Ana koyar da hardar kur’ani mai tsarki a kowace rana na wasu shafukan kur’ani, inda akan yin takara a da yamma da dare kuma akan koyar da wasu ilmomi na addini.
Baya ga hakan kuma akwai wasu shirye-shiryen da ak gudanarwa a kowace rana wadanda za su taimaka ma daliban da suke cikin shirin ta fuskar koyon harada da kuma sauran ilmomi na kur’ani.